Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Bai Kano, Alh Mukhtar Adnan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Bai Kano, Alh Mukhtar Adnan

  • Allah ya yiwa Sarkin Ban Kano Hakimin Danbatta Alh Mukhtar Adnan rasuwa.
  • Ya rasu yana da shekara 95 shi ne Basarake mafi dadewa a kan sarauta a hakiman Kano.
  • Ya kwashe shekara 65 yana sarauta a kasar Danbatta kafin rarraba masarautar Kano zuwa kaso biyar a 2019 inda yabar hakimchin Danbatta

Alh Mukhtar Adnan ya fito daga zuriyar Fulani Dambazawa, tsohon dan majalisar tarayya ta Lagos ne a 1952. Kuma shi ne kwamishinan ilimi na farko a Kano 1968.

Yana daga cikin mutum hudu masu zaben Sarakunan Kano. Ya zabi Sarki Muhammadu Inuwa a 1963 da Alh Ado Bayero 1963 da Malam Sunusi Lamido Sunusi ll 2014 da Kuma Sarkin Kano Aminu Ado Bayero 2019.

Alh Adnan Danbatta
Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigain Sarkin Bai Kano, Alh Adnan Danbatta Hoto: BBC
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Bayan shekara 65 kan gadon sarauta Sarkin Ban Kano, Adnan Mukhtar ya rasu a daren Juma'a

Shafin Dandalin Masarautun Arewa ta bayyana wasu abubuwa akan Marigayi Sarkin Bai din Kano:

1) Shi ne hakimi mafi dadewa a tarihin Kano

2) Ya gaji mahaifin sa, Sarkin Bai Adnan (Gazetteer of Dambatta, ta bayyana Adnan da cewa, wani gogaggen mutum ne mara kasala)

3) Mahaifin sa ne ya fara hakimcin Dambatta, tun bai zama Sarkin Bai ba, yana Dammaje hakimin Babura, aka dawo da shi Dambatta, bayan an cire Sarkin Bai Abdulkadir daga hakimin Danbatta, amma an bar masa sarautar sa, saboda samun sa da sakaci da sha'anonin mulki da na sharia.

4) Yana hakimin Dambatta, Sarkin Ban Kano, aka bashi Kwamishinan ilmi na jihar Kano.

5) Shi ne ya fara kirkiro da Kano Scholarship Board, Kano State Polytechnic, Audu Bako School of Agric da wasu manyan makarantun sikandire a jihar Kano.

6) A zamanin sa ilmin boko da na addini ya samu tagomashi kwarai. Sabida himmar sa, an samu yawaitar masu ilmin jami'a yan Kano.

Kara karanta wannan

Matashin Fasto ya yi garkuwa da babban Bishop na Katolika a jihar Imo

7) Sarkin Kano Bayero ya nada shi Sarkin Bai kuma dan majalisar Sarki yana da karancin Shekaru.

8) Tarihin sa ya tabbatar da cewa matasa na da kyakkyawar rawar da za su taka a sha'anin tafiyar da al'amurran al'umma da cigaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel