Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa
- Sabon salon da 'yan bindigan yankin jihar Niger suka fito da shi shine karbar fakitin sigari da sunkin wiwi a matsayin fansa
- A makonni biyu da suka gabata, 'yan bindiga sun kwashe jama'a a yankunan Zazzaga, Cibani da sauransu a karamar hukumar Munya ta jihar
- 'Yan uwan wadanda aka sacen sun kai garin masara, fakitin Maggi da jarkokin mai kafin a sako 'yan uwansu da aka sace
Niger - 'Yan bindiga da suka addabi yankunan karamar hukumar Munya ta jihar Niger suna tirsasa mazauna yankin wurin ba su fakitin sigari da sunkin wiwi domin fansar 'yan uwansu da suka sata.
Daily Trust ta ruwaito cewa, jama'a masu tarin yawa na yankunan Zazzaga, Cibani da sauransu da ke karamar hukumar Munya suna hannun masu garkuwa da mutane.
Wani mamba na kwamitin tsaro a yankin ya sanar da cewa, sun kai wadannan kayayyakin ga 'yan daban a ranar Talata kafin su sako wasu daga cikin wadanda aka sace.
"Dan uwan ka yana hannunsu, duk abinda za a yi domin samun a sako shi, ba za ka jinkirta ba. Akwai wasu yara da suka sace a wancan farmakin da suka kai gonaki. Iyayensu dole suka kai abinda suka bukata, an sako wasu daga ciki," yace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce 'yan bindigan sun bukaci garin masara, fakitin Maggi da jarkokin fetur wanda iyayensu suka kai musu, Daily Trust ta ruwaito hakan.
'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger
A wani labari na daban, yayin da ‘yan bindiga su ka kai farmaki garin Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja, sun halaka mafarauci sannan suka yi garkuwa da fiye da mutane 30.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da aukuwar lamarin, Daily Trust ta wallafa.
A cewarsa, lamarin ya auku da misalin 2am na Laraba inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun bi sawun ‘yan bindigan don ceto wadanda su ka yi garkuwa da su.
Sai dai, Sakataren karamar hukumar Munya, James Jagaba, ya sanar da wakilin Daily Trust ta wayar salula ya ce an yi garkuwa da mutane 68, har da mata da yara.
Asali: Legit.ng