Da duminsa: ISWAP sun saci fasinjoji 15 a Borno, sun iza keyarsu cikin dajin Sambisa

Da duminsa: ISWAP sun saci fasinjoji 15 a Borno, sun iza keyarsu cikin dajin Sambisa

  • Mayakan ta'addanci na ISWAP sun sace a kalla fasinjoji 15 a wurin kauyen Gumsuri da ke karamar hukumar Damboa ta jihar Borno
  • 'Yan ta'addan sun yi badda kama ne inda suka saka kayan sojoji tare da tsare motocin kan titi sannan suka iza keyar fasinjojin zuwa dajin Sambisa
  • Kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar, sun saci 15 tare da kyale mutum 2 daga cikin fasinjojin, daga ciki akwai ma'aikatan NGO

Borno - A kalla fasinjoji 15 ne miyagun da ake zargin mayakan ta'addancin ISWAP ne suka sace a Borno.

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, an sace jama'ar ne a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Da duminsa: ISWAP sun saci fasinjoji 15 a Borno, sun iza keyarsu cikin dajin Sambisa
Da duminsa: ISWAP sun saci fasinjoji 15 a Borno, sun iza keyarsu cikin dajin Sambisa
Asali: Original

Majiyar ta ce 'yan ta'addan sun kai farmaki ne wurin kauyen Gumsuri da ke karamar hukumar Damboa ta jihar.

Kara karanta wannan

Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda

Ya ce sun tare masu ababen hawa inda suka saka karfi wurin tasa keyarsu zuwa dajin Sambisa.

Daily Trust ta tattaro cewa, akwai wasu daga cikin ma'aikatan kungiyoyin taimakon kai da kai daga cikin wadanda aka sacen.

Da yawa daga cikin wadanda aka sace akwai matasa wadanda aka gano sun baro garin Damboa ne a kan hanyarsu ta zuwa Adamawa a ranar Laraba.

'Yan ta'addan da suka tare titunan, suna sanye ne da kayan sojoji.

"Abun takaici ne yadda 'yan ta'adda suka cigaba da aiwatar da miyagun ayyuka a kusa da dajin Sambisa. Mun samu rahotannin yadda miyagun suka sace a kalla fasinjoji 15 kusa da kauyen Gumsuri yayin da suka bar wasu biyu suka tafi.
“A kagauce suke wurin samun wadanda za su dinga aiwatar musu da miyagun ayyukansu. Sun yaudari mutane saboda sun saka kayan sojoji. Abun da takaici tare da bada tsoro,"majiyar tsaro ta sanar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Mummunan lamarin ya faru ne bayan miyagun 'yan ta'addan sun sace wani jami'in gwamnatin jihar Borno na ma'aikatar ayyuka wanda ke duba aikin titin da ake yi daga Chibok zuwa Damboa.

Masu satar mutanen sun kara da kwashe manyan motoci uku da ke kai kasa wurin aiki.

Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

A wani labari na daban, miyagun ƴan ta'addan kungiyar Islamic State in West Africa, ISWAP, sun sace ma'aikatan gwamnatin jihar Borno a ƙalla biyar, rahoton Daily Trust.

An sace ma'aikatan ne a ranar Laraba, a lokacin da suka saka ido a kan aikin ginin titin Chibok-Damboa.

Lamarin ya faru ne kusa da Wovi, a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Chibok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng