Jihohi da ranaku: Karo 15 da 'yan bindiga suka balle gidajen yari a Najeriya cikin shekara 1
A cikin shekara daya data gabata, mazauna gidajen gyaran hali 5,238 suka tsere daga gidaje daban-daban a fadin Najeriya, kamar yadda Premium Times ta kiyasta.
An samu irin hakan ta faru kashi 15 a cikin wannan lokacin, takwas daga ciki duk miyagun sun samu nasarar aiwatar da mugun nufinsu.
Balle gidan yarin Jos da aka yi a ranar Juma'a shi ne karshe. Hukumomin gidajen gyaran halin sun ce an sake damko mutum takwas da suka tsere.
Tabarbarewar tsaro a kasar nan yana daga cikin dalilin da ya ke kawo balle gidajen yari, garkuwa da mutane da tafka ta'asar 'yan bindiga.
Ga jerin jihohi da ranakun da aka dinga balle gidajen gyaran hali a Najeriya a cikin shekara daya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Yan Bindiga Sun Sace Malaman Addinin Musulunci 2 Bayan Cika Cikinsu Da Teba Da Miya Da Matar Malamin Ta Dafa
Edo
October 19, 2020: Mataimakin shugaban gidan gyaran halin Oko, West Amayo, ya ce wurin karfe 9 na safe aka yi yunkurin balle gidan amma ba a yi nasara ba.
October 21, 2020: Bayan kwana biyu da yunkurin balle gidan gyaran halin Oko, 'yan bindiga sun balle gidan gyaran halin Benin da ke kan titin Benin zuwa Sapele.
Jimillar mutum 1,993 ne suka tsere daga gidajen biyu.
April 15, 2021: Jami'an hadin guiwa daga NSCDC na rundunar jihar Edo tare da gidajen gyaran hali sun dakile yunkurin balle gidan da ke Ubiaja, karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas.
October 29, 2021: Wani rikici ya balle tsakanin mazauna gidan yarin Benin kuma wasu sun yi yunkurin balle gidan, amma kokari da taimakon jami'an tsaro yasa zaman lafiya ya dawo.
Ondo
October 22, 2020: Kusan mazauna gidan gyaran hali 58 ne suka tsere daga karamar hukumar Okitipupa a jihar Ondo bayan 'yan daba sun kutsa. Maharan sun tarwatsa kayayyakin gidan tare da raunata ma'aikatan a farfajiyar.
Lagos
October 22, 2020: 'Yan sanda da sojoji sun bankado harin balle gidan gyaran halin Ikoyi. A yayin farmakin, an harbi wasu mazauna gidan gyaran halin da suka yi yunkurin fita.
Abia
October 22, 2020: An bankado yunkurin balle gidan gyaran halin Afara da ke Umuahia sakamakon kokarin sojoji, 'yan sanda da jami'an NSCDC.
Jami'an tsaron sun dinga harbi tare da watsa barkonon tsohuwa a iska domin watsa 'yan ta'addan.
Delta
October 22, 2020: An kashe jami'in gidan gyaran hali a Warri da ke Delta a wani yunkurin balle gidan da mazauna suka yi. Sun bankawa kofar shiga wuta tare da ofisoshin gidan.
Imo
April 4, 2021: 'Yan bindiga sun kai farmaki gidan gyaran halin Owerri kuma sun saki mutum 1,844. Sai dai jami'ai sun ce an mayar da mutum 84 gidan.
Bauchi
April 9, 2021: Jami'ai biyu na gidan gyaran hali da ke Bauchi sun samu miyagun raunika bayan zanga-zanga da ta balle a gidan. Biyar sun jigata amma babu wanda ya samu nasarar tserewa.
Kano
April 22, 2021: Jami'an tsaro sun bankado yunkurin balle gidan gyaran halin Kurmawa da ke cikin fadar sarkin Kano.
Babu wanda ya mutu sai dai jami'an tsaron sun dinga sakin harbi domin tsorata miyagun. Mai magana da yawun gidan a Kano, Musbahu Lawal, ya ce wasu 'yan gidan ne suka shirya balle gidan.
Kogi
September 13, 2021: Miyagun 'yan bindiga sun yi yunkurin balle gidan yarin Kabba da ke jihar Kogi inda suka kashe jami'ai biyu tare da sakin mutum 240.
A kalla mutum 114 daga cikin 240 na gidan aka sake kamawa bayan shugaban hukumar, Haliru Nababa ya bayar da umarnin damko dukkan wadanda suka tsere.
Oyo
October 22, 2021: Miyagun sun kai farmaki gidan gyaran hali na Abolongo kuma mutum 837 ne suka tsere, amma ministan harkokin cikin gida ya ce an sake kama 262.
Jos
July 19, 2021: Mutum hudu ne suka tsere daga matsakaiciyar gidan yarin Jos.
November 28, 2021: Wannan shi ne kokarin balle gidan yari na karshe wanda ya auku a ranar Lahadi bayan 'yan bindiga sun tsinkayi matsakaiciyar gidan yarin da ke Jos.
Sun saki mutum 262 kuma a kalla mutum goma ne suka mutu sakamakon arangamar.
Asali: Legit.ng