Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

  • Shugaban hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta gano ayyuka 257 da aka kwafo daga cikin kasafin kudin shekarar 2021
  • Bolaji Owasanoye ya sanar da yadda wadannan ayyukan da aka kwafo za su iya lamushe kudi har N20.138 biliyan
  • A cewarsa, hukumar ta bibiyi manyan ayyuka 966 masu darajar N310 biliyan daga 'yan kwangila 67 wadanda aka yi watsi da su

Bolaji Owasanoye, shugaban hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta ce ayyuka 257 da za su kai darajar N20.138 biliyan aka kwafa daga kasafin kudin shekarar 2021.

Shugaban hukumar ICPCn yayin jawabi a taro karo na uku kan disashe rashawa a aikin gwamnati a kasar nan mai taken “Corruption and the Cost of Governance: New Imperatives for Fiscal Transparency”, ya ce hukumar ta bibiyi ayyuka 1083 a fadin kasar nan ban da Borno da Zamfara saboda matsalar tsaro, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC
Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

TheCable ta ruwaito cewa, ya sanar da cewa yayin binciken, ICPC ta tirsasa 'yan kwangila 67 sun koma aikin kuma sun tabbatar da kammaluwar ayyuka 966 masu darajar N310 biliyan wadanda aka watsar a baya.

"Bincikenmu ya nuna cewa irin wannan tsarin rashawan ne ke durkushe manyan ayyukan jama'a da gwamnati ke yi, ya ke kara yawan kudin da ake kashewa kuma ya ke lalata darajar kudi," Owasanoye yace.
“Wadannan matsalolin sun hada da rashin duba ayyuka da aka saka a yi, karya wurin tabbatar da kammaluwar kwangila, kin kammala kwangila da gangan, waskar da kudi da kuma kayan gwamnati da ma'aikatan gwamnati ke yi da sauransu.
"Sauran kalubalen sun hada da kwafar ayyuka daga kasafin kudi. ICPC ta gano ayyuka 257 da za su kai darajar N20.138 biliyan wadanda aka kwafo daga kasafin kudin 2021.

Kara karanta wannan

'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblisa ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

"Hakan yasa muka mika shawara ga mai girma ministan kudi wanda ya dace a gaggauta daukan mataki domin dakile asara."

Kasafin kudin 2022: N31m kudin man Janareton Aso Rock, N22.07m na Gas din girki, N33m na littafai

A wani labari na daban, karin bayanai kasan daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya na nuna cewa za'a kashe miliyoyin kudi don tabbatar da akwai wuta koda yaushe a fadar shugaban kasa.

Bayanai da Legit.ng ta tattaro cikin kasafin kudin ya nuna cewa ana bukatan N30.67 million domin sayan man feturin Janareton fadar shugaban kasa.

Hakazalika kasafin kudin ya bayyana cewa za'a yi amfani da N22.07 million wajen sayar iskar Gas na girki a 2022. Bugu da kari, kasafin kudin fadar shugaban kasa ya nuna cewa za'a kashe N66.49million kan maktaban Aso Rock.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng