Kasafin kudin 2022: N31m kudin man Janareton Aso Rock, N22.07m na Gas din girki, N33m na littafai

Kasafin kudin 2022: N31m kudin man Janareton Aso Rock, N22.07m na Gas din girki, N33m na littafai

  • Legit.ng ta cigaba da kawo muku bayanai kan daftarin kasafin kudin 2022 da Buhari ya gabatar gaban majalisa
  • A kasafin kudin 2022, gwamnatin tarayya na shirin kashe N16.39 trillion
  • Cikin wannan kudi, gwamnati zata karbi bashin sama da N5tr

Karin bayanai kasan daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya na nuna cewa za'a kashe miliyoyin kudi don tabbatar da akwai wuta koda yaushe a fadar shugaban kasa.

Bayanai da Legit.ng ta tattaro cikin kasafin kudin ya nuna cewa ana bukatan N30.67 million domin sayan man feturin Janareton fadar shugaban kasa.

Hakazalika kasafin kudin ya bayyana cewa za'a yi amfani da N22.07 million wajen sayar iskar Gas na girki a 2022.

Bugu da kari, kasafin kudin fadar shugaban kasa ya nuna cewa za'a kashe N66.49million kan maktaban Aso Rock.

Kara karanta wannan

A kasafin kudin 2022, Buhari ya bukaci N5.23bn na gyaran fadar shugaban kasa

Cikin wannan kudi, za'a yi amfani da N25.28 million wajen zamanantar da dakin ajiye litattafai.

Bayan haka kuma a sayi sabbin litattafai na N33.23million.

Kasafin kudin 2022: N31m kudin man Janareton Aso Rock, N22.07m na Gas din girki, N33m na littafai
Kasafin kudin 2022: N31m kudin man Janareton Aso Rock, N22.07m na Gas din girki, N33m na littafai
Asali: UGC

Wasu abubuwan da ke kunshe cikin kasafin kudin 2022

Za'a salwantar da N20.18 million wajen ayyukan wasanni da motssa jiki, yayinda za'a kashe N35.95 million wajen sayen sabbin kayayyakin wasanni da shakatawa.

Mataimakin shugaban kasa kuwa zai kashe N5.48 million wajen kayayyakin wasanni da motsa jiki kuma za'a kashe N2.35 million don sayar iskar gas na girki.

Kasafin Kudi: Za'a kashe N35m wajen kwashe Masai a Aso Villa, a 2022

Shugaba Buhari ya bukaci N35.41 million don yashe shaddar fadar shugaban kasa.

Wannan na kunshe cikin daftarin kasafin kudin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis, 7 ga Oktoba, 2021.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2022: Buhari ya bukaci N644.3m matsayin kudin abinci, N76.6m na kudin haya

Kudin kwashe masai mai lamba 22020206 ya kasance abinda ake bukata koda yaushe don kwashe masai a fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng