Hukumar Kwastam ta kama wata mota makare da tsabar kudi a Katsina
- Rundunar kwastam a jihar Katsina ta kame wasu haramtattun kaya da yawa a cikin wannan watan na Nuwamba
- Daga ciki, an kame wata mota makare da kudaden da suka haura Naira miliyan 71 a kan iyaka a jihar ta Katsina
- Hakazalika, rundunar ta shaidawa manema labarai irin nasarorin da ta samu cikin watan Nuwamban bana
Katsina - Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) a jihar Katsina ta ce ta cafke wata mota makare da kudi sama da Naira miliyan 71 da ake zargin na harkallar miyagun kwayoyi ne, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mukaddashin Konturola na rundunar, Dalhat Wada-Chedi, ya shaida wa manema labarai a Katsina ranar Litinin cewa an kama kudaden ne a farkon watan Nuwamba.
A cewarsa:
“Mun kama kudin da motar kuma mun kama direban motar a kan titin Katsina zuwa Jibia wanda ke cikin sahun gaba da rashin tsaro ya shafa.
“An kama wannan kudi ne a kan iyakar, a bayan motar Toyota Corolla biyo bayan kokarin da jami’an mu suka yi a kan wannan aiki.
“Kamar yadda kuka sani har yanzu iyakokin suna rufe, kuma duk wanda ya bi ta kan iyaka dole ne ya bayyana kudin da suka kai sama da dala 10,000.
“Mun kawo kudin da wanda ake zargin da kuma motar, kuma mun ajiye kudin a babban bankin Najeriya CBN bayan mun kai rahoto ga hedkwatar mu.
“Mun bayar da belin wanda ake zargin saboda har yanzu ana ci gaba da bincike; karshe ma mun mayar da shari’ar zuwa hedikwata."
Mista Wada-Chedi ya kuma shaida wa manema labarai cewa, rundunar ta kuma kama fakiti 230 na tabar wiwi da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 18.1 a watan Nuwamba, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.
A cewarsa:
“An kama tabar wiwi a cikin wata babbar mota kuma jimillar kimar tabar wiwi din da aka kama ta kai Naira miliyan 25.9."
Ya kara da cewa rundunar ta kama motoci takwas da darajarsu ya kai Naira miliyan 14.4 kuma a watan Nuwamba.
Hakazalika rundunar ta kama shinkafa, taliya, man gyada, kanwa da magunguna a cikin watan Nuwamba.
Ya kara da cewa:
“Mun kuma kama kwalayen man shafawa na kasashen waje, jarakunan man fetur, dizal, buhunan kayan sawa na jarirai.
“Hakazalika, an kama wasu wukake da jakuna iri-iri guda uku da buhunan aya da darajarsu ya kai Naira miliyan 46.5 a watan Nuwamba."
Mista Wada-Chedi ya kara da cewa:
“A cikin watan Nuwamba, mun yi nasarar cafke mutane biyar da ake zargi da kuma kayayyaki daban-daban da suka haura Naira miliyan 176.4."
Ya kuma bayyana nasarorin da hukumar ta samu sakamakon namijin kokarin da rundunar da jami’anta ke yi, ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba su goyon bayan da ya dace.
Hukumar kwastam ta yi ram da tulin Tramadol a filin jirgin saman dakon kaya
A wani labarin, jami’an hukumar kwastam ta Najeriya a ranar Talata sun kama kwayoyin Tramadol kimanin miliyan 1.5 a filin jirgin saman dakon kaya na jihar Legas, Channels Tv ta ruwaito.
Jami’an hukumar kwastam ta yankin Murtala Mohammed ne suka kama kayayyakin a rumfar shigo da kaya ta SAHCO dake Legas.
Da yake jawabi ga manema labarai, kwamandan yankin Murtala Mohammed, Sambo Dangaladima ya ce duk da cewa ba a kama wanda ake zargi ba, an kama kayayyakin da kudinsu ya kai Naira miliyan 92.3 domin ci gaba da bincike.
Asali: Legit.ng