Mutuwa rigar kowa: Dan majalisar dokoki a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
- Mamba a majalisar dokokin jihar Filato, Henry Longs, ya rigamu gidan gaskiya da yammacin ranar Lahadi da ta gabata
- Rahotanni sun bayyana cewa Longs, wanda ke wakiltar mazaɓar Pankshin ta kudu ya mutu ne bayan an masa tiyata a kafa
- Shugaban kwamitin labarai na majalisar Filato, Philip Dasun, yace wannan rashi da suka yi zai taba su, kuma za su yi kewar marigayin
Plateau - Wani mamba a majalisar dokokin jihar Filato dake arewacin Najeriya, Henry Longs, ya rigamu gidan gaskiya.
Jaridar Punch ta rahoto cewa marigayi Honorabul Longs ya rasu ne a Jos da yammacin ranar Lahadi 28 ga watan Nuwamba, 2021.
Kafin rasuwarsa, Longs shine ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Pankshin ta kudu a majalisar dokokin jihar Filato karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Kazalika rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya mutu ne jim kaɗan bayan an masa tiyata a ƙafa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Majalisa ta tabbatar da rashin Longs
Shugaban kwamitin yaɗa labarai, Philip Dasun, shine ya tabbatar da mutuwar abokin aikinsa ga manema labarai ranar Lahadi.
Honorabul Dasun yace:
"Eh, dagaske ne mun yi rashin ɗaya daga cikin mambobin mu da yammacin nan. Ɗan majalisa mai wakiltar Pankshin ta kudu, Henry Longs, shine muka rasa."
"Yana da wata damuwa a ɗaya daga cikin kafafunsa, hakan yasa yaje domin a yi masa tiyata. Amma abun takaicin shine bai iya tashi ba."
"Mutuwarsa babban abin takaici ne a gare mu da jimami, kuma tabbas zamu yi matukar kewarsa."
A wani labarin kuma Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai
Wata daliba dake ajin karshe a jami'ar Bayero dake Kano ta rasa rayuwarta a ɗakin kwanan ɗalibai bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa, Binta Isa, ta faɗa wa abokan zaman ta a ɗaki cewa tana jin ciwan kirji, tana fara sallah ta rasu.
Asali: Legit.ng