Jami'an tsaro sun titsiye 'yan bindigan da suka yi yunkurin balle gidan yarin Jos a cikin gidan
- Jami'an tsaro tare da masu tsaron gidan gyaran halin garin Jos a jihar Filato sun titsiye 'yan bindiga da suka kai farmaki gidan a cikin gidan gyaran halin
- Kamar yadda kakakin hukumar ya sanar, ya ce maharan sun isa wurin karfe 5 na yammaci kuma sun budewa masu tsaron gidan wuta domin su balle shi
- Sai dai sauran cibiyoyin tsaro sun hanzarta kai musu dauki inda a halin yanzu suka mamaye gidan kuma suka ritsa da maharan a cikin gidan
Jos, Filato - A halin yanzu, jami'an tsaro sun titsiye miyagun 'yan bindigan da ke kai farmaki gidan gyaran halin garin Jos a ranar Lahadi a cikin gidan.
'Yan bindiga sun tsinkayi gidan da tarin yawansu inda suka dinga harbe-harbe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Jeff Longdiem, mai magana da yawun gidan gyaran halin, ya tabbatar da wannan cigaban a wata takarda da ya aike wa Daily Trust.
Tun farko Daily Trust ta ruwaito cewa, an dinga jin harbe-harbe a gidan gyaran halin Jos.
Mai magana da yawun gidan ya yi bayanin cewa:
"Maharan sun isa gidan gyaran halin wurin karfe biyar da mintuna ashirin kuma da gaggawa suka isa kofar shiga inda suka budewa jami'an tsaron wuta.
"Duk da sun samu shiga cikin gidan, a halin yanzu an ritsa da su saboda sauran cibiyoyin tsaro sun gaggauta kawo mana dauki kuma sun mamaye dukkan gidan.
“Sauran cibiyoyin taimakon gaggawa sun hanzarta kawo mana dauki. A halin yanzu komai ya lafa saboda masu ruwan wutan sun ji martanin da ya fi nasu daga hukumomin tsaro. Duk abinda ke faruwa za mu sanar da manema labarai," takardar tace.
Karar harbe-harbe na cigaba da tashi a gidan yarin Jos
A wani labari na daban, jaridar Dailytrust ta rahoto cewa yanzu haka ana cigaba da jin karar harbe-harbe a gidan gyaran halin Jos, jihar Filato. Rahotanni sun bayyana cewa karar harbe-harben ya fara tashi ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi.
A halin yanzun jami'an tsaro sun mamaye baki ɗaya ilahirin yankin, inada suke cigaba da kula da zirga-zirgan mutane a yankin.
Da muka tuntuɓi kakakin hukumar gyaran hali NCoS reshen jihar Filato, Jeff Longdiem, kan abinda ke faruwa, ya yi alkawarin zai neme mu daga baya.
Asali: Legit.ng