Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi
- Wasu 'yan bindiga sun hallaka mazauna kauyen Durbi a jihar Filato, yayin da mazauna ke kokarin fatattakarsu
- An ruwaito cewa, mutane biyu ne aka kashe a sabon harin, inji wata majiya daga kauyen da abin ya faru
- Mataimakin shugaban karamar hukumar Jos ta gabas ya tabbatar da faruwar harin ya kuma ce ana kokarin shawo kan lamarin
Filato - An harbe wasu mutane biyu mazauna kauyen Durbi da ke gundumar Shere a karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato yayin da suke fafatawa da masu garkuwa da mutane.
Maharan, a cewar mazauna garin, sun bude wuta kan mutanen da ke bibiyarsu daga maboyarsu.
Wasu da dama kuma an ce sun samu raunuka a lamarin.
Wadanda suka mutun dai sun hada da Peter Inyam da Arin Kaze.
Wani mazaunin garin ya ce:
"Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, lokacin da wani manomi ya je diban zaitun, ya kuma ga wasu ‘yan bindiga a kan tsauni.
“Ya koma gida a guje ya sanar da al’umma abin da ke faruwa sai jama’a suka yi gaggawar zuwa tsaunuka domin su fatattake su.
“A cikin haka ne aka kashe biyu daga cikin mutanen kauyen.”
Hon. Ishaku Ayuba Ajang, mataimakin shugaban karamar hukumar Jos ta gabas, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya kara da cewa an hada jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a yankin.
ASP Ubah Gabriel, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, bai amsa kira da kuma sakon SMS da wakilin Daily Trust ya aike masa ba.
'Yan bindiga na ci gaba da barna a wasu yankunan Arewacin Najeriya, lamarin da ke kara sanya tsoro a zukatan mazauna.
Yayin da gwamnatoci ke ci gaba da neman hanyoyin dakile hare-haren 'yan bindiga ta hanyar soja, malamin addinin Islama, Sheikh Gumi na kan ra'ayin cewa, hakan ba zai haifar da da mai ido ba.
Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano
A wani labarin, wani kasurgumin ɗan fashi da makami, ɗan kimanin shekara 18, Sabitu Ibrahim, wanda yana cikin jerin waɗan da yan sanda ke nema, ya shiga hannu a Kano.
Vanguard tace kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, shine ya tabbatar da nasarar ga manema labarai.
Ya kuma kara da cewa hukumar yan sanda ta damke wasu mutum.biyu dake siyan kayayyakin sata a jihar.
Asali: Legit.ng