Ana daf da yi musu yankan rago: Amotekun sun ceto makiyaya fulani 2 da wasu fulanin suka yi garkuwa da su
- Jami'an tsaro na Amotekun a jihar Ondo sun ceto wasu makiyaya fulani yaya da kani da wasu fulanin suka sace su
- Jami'an Amotekun din sun isa dajin ne yayin da masu garkuwan ke shirin yi wa makiyayan biyu yankan rago
- Sun yi nasarar ceto mutanen biyu sannan suka kama mutum daya daga cikin masu garkuwa da mutanen
Ondo - Hukumar tsaro ta jihar Ondo da ake fi sani da Amoketun Corp, ta ceto Fulani makiyaya biyu da 'yan uwansu makiyaya suka yi garkuwa da su, The Punch ta ruwaito.
Wasu gungun masu garkuwa da mutane ne suka sace makiyayan a Supare Akoko, karamar hukumar Akoko kudu maso yammacin jihar kwanakin baya.
Kwamandan hukumar a jihar, Cof Adetunji Adeleye, ya bayyana sunayen wadanda aka ceto din - Musa Ibrahim da Amidu Ibrahim.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yi bayanin cewa an daure su a jikin bishiya, ana daf da yi musu yankan rago sai jami'ansa suka isa wurin.
Adeleye, ya kara da cewa mutum daya ne kawai cikin masu garkuwan, Sidi Amodu kawai aka kama.
A cewar shugaban na Amotekun, a lokacin da jami'ansa suka isa wurin, bata garin, kimanin su bakwai sun tsere, sun bar Amodu wanda a lokacin yana barci ne.
Ya ce:
"Wannan makiyaya ne suka sace yan uwansu makiyaya fulani. Mutane biyun da Amotekun ta ceto yaya da kani ne; Musa Ibrahim da Amidu Ibrahim kuma makiyaya ne.
"An sace su ne a Supare Akoko an kwace musu kayansu masu muhimmanci. An daure su a bishiya za a yanka su kafin mutanen mu suka isa wurin. Mun shiga dajin da suke boye sun yi nasarar kama daya daga cikin bata garin.
"Ya amsa aikata laifin ya ce su bakwai suka taho daga jihohin Edo da Kogi. Ya ce mutum takwas suka sace kafin wadannan. Ya ce sauran sun gudu ne lokacin da jami'an Amotekun suka iso don kada a kama su."
Wanda ake zargi da garkuwan, Sidi Amodu ya yi ikirarin cewa musamman ya baro jihar Kogi domin ya taho yin garkuwa da mutane kuma ya dakko hayan shanu amma ba nasu bane.
Ya kara da cewa sun yi wa mutane da dama fashi a wurare daban-daban musamman inda titi ba shi da kyau.
Wadanda aka ceto sun bayyana halin da suka shiga
Makiyayan biyu da aka ceto sun ce sun sha duka da azaba a hannun bata garin.
Musa ya ce:
"Sun azabtar da mu sun fada mana mu kira yan uwan mu su kawo kudin fansa kafin a sake mu idan ba haka ba za su kashe mu. Sun mana duka suna daf da kashe mu sai Jami'an Amoketun suka iso dajin."
Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su
A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.
Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.
Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.
Asali: Legit.ng