Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja
- Muhammadu Buhari ya ba shugabannin tsaro umarnin kawar da duk wasu ‘yan bindiga daga titin Abuja zuwa Kaduna da sauran wurare
- Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Alhamis a karshen taron da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaro kasa a Abuja
- Aregbesola ya ce shugaban kasan ya ba shugabannin tsaro, hukumomin binciken sirri da duk wasu masu ruwa da tsaki umarnin tsayawa tsayin-daka wurin kawar da ta’addanci a kasar
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaron kasar nan da su kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a kasa musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis bayan wani taro da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaron kasa, NSC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa shugaban kasan ya ba ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro ciki har da jami’an binciken sirri umarnin kada su zauna har sai sun kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, amsar kudaden fansa da sauransu a Najeriya.
Zaman lafiya ya dace da ‘yan Najeriya inji Buhari
Ya ce:
“Shugaban kasa ya ce har yanzu ba mu kai wurin da ya dace mu kai ba. ‘Yan Najeriya sun fi dacewa da zama cikin salama kuma ba za mu zauna ba har sai mun samu nasara.”
Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda manema labarai su ka tambayi Aregbesola idan a taron an tattauna akan rashin tsaron titin Abuja zuwa Kaduna, inda ya bada amsa da eh.
Ya kara da bayyana yadda aka bukaci ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro da su tsananta sintiri don binciko ‘yan bindiga a tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
A cewarsa:
“Ya umarci duk wasu jami’an da suke da alhakin samar da tsaro da bin dokoki su zage damtse wurin kawo saukin farmaki ko kuma kawar da ta’addancin gabadaya a kasar nan.”
‘Yan sanda ne masu alhakin bayar da tsaron cikin gida
Manema labarai sun bukaci sanin jami’an tsaron da aka daura wa alhakin zama jagororin kawo karshen rashin tsaro, inda ya amsa da cewa ‘yan sanda ne ke da alhakin yaki da rashin tsaron cikin gida.
Ya kara da cewa Buhari ya bayar da umarnin ganin bayan duk wasu ‘yan ta’addan da suke kawo cikas ga tsaro a Najeriya daga ko wanne bangare.
“A yau kwamitin ta dauki tsauraran matakai kuma zan iya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa bisa umarnin shugaban kasa, za su yi gaggawar ganin canji a kasar nan,” a cewar Aregbesola.
Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna
'Yan bindiga sun kashe Sagir Hamidu, tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a shekarar 2019, a babban hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Marigayin dan siyasan ya nemi kujerar gwamnan ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin kasa.
Maharan sun bindige shi har lahira ne yayin da suka bude wuta kan matafiya a kusa da Rijana misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng