'Yan sanda sun yi ram da dan fashin da yayi basaja kamar makiyayi
- 'Yan sanda sun damke wani bayerabe mai suna Biodun Rasheed ya na fashi da makami amma da shigar Fulani makiyaya
- Rundunar jihar Ogun ta sanar da yadda 'yan fashin suka budewa jama'a wuta amma 'yan sandan suka gaggauta kai musu dauki
- 'Yan fashin sun cafke Biodun wanda a halin yanzu ya ke taimaka wa 'yan sandan wurin damko sauran 'yan tawagarsa
Ogun - Wani mutum da ake zargi da fashi da makami mai suna Biodun Rasheed, wanda yayi shiga tamkar makiyayi ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Ogun.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun yi ram da wanda ake zargin yayin da ya ke tsaka da fashi da makami, Daily Trust ta ruwaito hakan.
'Yan sandan da ke aiki da ofishin Kemta a karamar hukumar Odeda ta jihar sun samu kiran gaggawa kan cewa 'yan fashi da makami na barna a mile 6 da ke kan titin Ajebo a garin Abeokuta.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi a ranar Alhamis ta sanar da manema labarai cewa, bayan kiran gaggawan ne DPO ya aike tawagar sintiri.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ruwaito cewa, CSP Opebiyi Sunday, ya hanzarta aika tawagar sintiri wadanda suka hadu da jami'an sintiri da kuma So Safe Corps.
"Bayan ganin jami'an tsaron, 'yan fashin sun tsere amma 'yan sandan sun bi su inda suka damke wani Biodun Rasheed wanda yayi shiga kamar Fulani makiyayi domin ya boye asalinsa," yace.
Oyeyemi ya ce wanda ake zargin "yanzu haka ya na taimakawa 'yan sanda wurin cafko sauran 'yan kungiyarsu."
A cewarsa, kwamishinan 'yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a gaggauta mika wanda ake zargin hannun runduna ta musamman ta bincike domin su cigaba da aikinsu.
Jami'an kwastam sun kwace tirela 12 ta shinkafa da miyagun kwayoyi a Ogun
A wani labari na daban, jami'an hukumar kwastam ta kasa, reshen jihar Ogun ta kama buhu 7,311 na shinkafar gwamnati wacce aka loda a tireloli 12 a jihar. Har ila yau, ta kama fakiti 124 da sunki 164 na wiwi mai nauyin 167kg, Punch ta ruwaito.
Shugaban hukumar na yankin, Dera Nnadi, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawa da manema labarai a ofishin NCS da ke Abeokuta, babban birnin jihar.
Shugaban ya bayyana cewa, hukumar ta cafke wasu mutum biyu wadanda ke kokarin kai kwayoyi Ijebu-Ode da ke kan hanyar kudu maso gabas.
Asali: Legit.ng