'Yan bindiga sun sace fasinjoji 5 a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa a Neja

'Yan bindiga sun sace fasinjoji 5 a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa a Neja

  • Wasu da ake kyautata zaton yan bindiga ne sun sace wasu fasinjoji biyar a jihar Neja
  • Fasinjojin suna hanyarsu na dawowa ne daga kasuwar Beji suka fada hannun miyagun
  • Sakataren Gwamnatin Neja, Ahmed Matane ya ce gwamnatin jihar za ta tura jami'an tsaro don ceto su

Wani rahoto daga The Nation ta ce 'yan bindiga sun sace mutane biyar a kan hanyar Beji - Manta a karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger.

An gano cewa wadanda aka sace suna kan hanyarsu ne na dawowa daga kasuwar Beji a yayin da yan bindigan suka tare su sannan suka yi awon gaba da su.

'Yan bindiga sun sace fasinjoji 5 a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa a Neja
Yan fashin daji sun sace mutane biyar a jihar Neja. Hoto: The Punch
Asali: UGC

An sanar da Sakataren Gwamnatin Jihar Niger, SSG, Alhaji Ahmed Matane afkuwar lamarin yayin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo da The Nation ta bibiya.

Kara karanta wannan

Zamfara: Gwamnati ta rufe wasu gidajen biredi da man fetur da ke yi wa 'yan bindiga aiki

Mai kirar wayan, Umar, ya shaidawa SSG din cewa yana son ya sanar da shi afkuwar lamarin ne domin hukumomin tsaro ba su san abinda ya faru ba.

Martanin SSG din

Sakataren gwamnatin ya nuna damuwarsa kan yadda abubuwa da dama ke faruwa dangane da sace mutane amma ba a sanar da hukumomi ta hanyoyin da suka dace.

Ya ce gwamnatin jihar bata da masaniya kan sace mutanen amma tunda yanzu ta sani za ta dauki mataki nan take.

"Wannan na daga cikin abin da muke fada na rashin kai rahoto. Sai yanzu na ke jin afkuwar wannan, ba mu san an sace mutane ba a hanyar Beji-Manta. Amma tunda yanzu mun samu zamu dauki mataki a kai," in ji shi.

Ya yi kira ga mutanen su rika takatsantsan wurin bin wannan hanyar musamman ranar cin kasuwanni.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Har wa yau, ya gargadi manoma su rika kulawa sosai yayin da za su tafi gonakinsu domin masu garkuwar sun bullo da sabuwar dabara ta ajiye babur dinsu su shiga gonar da kafa su sace manoma.

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

A wani labarin, jami'an rundunar yan sandan jihar Ogun sun kama mutum biyar cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane da ke adabar Obadda Oko da kewaye a karamar hukumar Ewekoro na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An kama wadanda ake zargin - Aliu Manya, Usman Abubakar, Abayomi Olayiwola, Nasiru Muhammad da Bello Usman bayan yan sandan hedkwata da ke Obada Oko sun samu bayanai.

Daily Trust ta rahoto cewa an tsegunta wa yan sandan cewa an hangi wasu mutane kan babura biyu a cikin daji da ke Eleja kusa da Obada Oko misalin karfe 8 na daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164