Za mu rabawa matan aure a Najeriya rishon girki guda 774,000: Ministar Harkokin Mata

Za mu rabawa matan aure a Najeriya rishon girki guda 774,000: Ministar Harkokin Mata

  • Yayinda kudin Gas na girki yayi tashin gwauron zabo, Gwamnatin tarayya na shirin nemanwa yan Najeriya sauki
  • Ministar harkokin mata ta bayyana shirin da gwamnati keyi na samawa matan karkara rishon girki
  • Ministar Yanayi kuwa ta yi kira ga iyaye mata su rage amfani da itace wajen girki saboda yana da illa ga su da yaransu kuma har kisa yana yi

Abuja - Gwamatin tarayya ta bayyana cewa tana shirin fara rabawa matan rishon girki a fadin kananan hukumomin Najeriya 774.

Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta bayyana hakan ranar Laraba yayin taron kaddamar da horo da hukumar makamashin Najeriya (ECN) ta shirya, rahoton Daily Trust.

Ministar ta mika godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari bisa amincewa da wannan shiri

Tace:

"Mun fahimci mata da yawa na mutuwa, saboda haka muna son tabbatar da cewa kowace karamar hukuma ta samu rishon girki 1000."

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

Ta ce an shirya taron ne domin ilmantar da matan karkara da wayar da kansu saboda su ke shan wahalan yin girki da itace a Abuja.

Ta kara da cewa wannan zai taimaka wajen yakar sauyin yanayi.

Rishon girkin Ministar Harkokin Mata
Za mu rabawa matan aure a Najeriya rishon girki guda 774,000: Ministar Harkokin Mata

Hayakin itacen girki na kashe akalla mutum 90,000 kowace shekara a Najeriya, Ministar Yanayi

A watar Oktoba, Ministar yanayi ta bayyana cewa hayakin itacen girki na kashe sama da yan Najeriya 90,000, musamman mata da kananan yara a kowace shekara.

Ministar Yanayi, Sharon Ikeazor, ta bayyana hakan a Abuja ranar Talata, a taron kungiyar wayar da kai kan girkin zamani, rahoton DailyTrust.

Ta bayyana cewa:

"Dogaro kan itace wajen girki na daura nauyi kan bishiyoyi a daji."
"Wannan na da hadari kan lafiyar masu amfani da shi, musamman mata dake girki tare da yaransu."

Ta ce shekara bayan shekaru, ma'aikatar yanayi na taimakawa wajen aiwatar da shirye-shiryen samar da hanyoyim girkin zamani domin rage tashin hayakin masu illa ga sararin samaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel