Hayakin itacen girki na kashe akalla mutum 90,000 kowace shekara a Najeriya, Ministar Yanayi

Hayakin itacen girki na kashe akalla mutum 90,000 kowace shekara a Najeriya, Ministar Yanayi

  • Ministar Yanayi ta yi kira ga iyaye mata su rage amfani da itace wajen girki
  • A cewarta, hayakin itacen na illa ga su da yaransu kuma har kisa yana yi
  • Ministar ta kara da cewa hayakin na da illa ga sararin samaniya

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa hayakin itacen girki na kashe sama da yan Najeriya 90,000, musamman mata da kananan yara a kowace shekara.

Ministar Yanayi, Sharon Ikeazor, ta bayyana hakan a Abuja ranar Talata, a taron kungiyar wayar da kai kan girkin zamani, rahoton DailyTrust.

Ta bayyana cewa:

"Dogaro kan itace wajen girki na daura nauyi kan bishiyoyi a daji."
"Wannan na da hadari kan lafiyar masu amfani da shi, musamman mata dake girki tare da yaransu."

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Gwamnatin Neja ta ce za ta sa kafar wando daya da masu ba 'yan bindiga bayanai

Ta ce shekara bayan shekaru, ma'aikatar yanayi na taimakawa wajen aiwatar da shirye-shiryen samar da hanyoyim girkin zamani domin rage tashin hayakin masu illa ga sararin samaniya."

Hayaki itacen girki na kashe akalla mutum 90,000 kowace shekara a Najeriya, Ministar Yanayi
Hayaki itacen girki na kashe akalla mutum 90,000 kowace shekara a Najeriya, Ministar Yanayi
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel