Gwamnoni da wasu manyan Arewa sun kai ziyarar jaje inda bene ya ruguje a Legas

Gwamnoni da wasu manyan Arewa sun kai ziyarar jaje inda bene ya ruguje a Legas

  • Arewa maso yamma a Najeriya sun ziyarci jihar Legas domin jajantawa wadanda lamarin rugujewar bene ya shafa
  • Gwamnan Kano, Ganduje da na Katsina Masari ne suka Kai ziyarar a madadin gwamnonin yankin Arewa maso yamma a Najeriya
  • Hakazalika, a tawagar tasu akwai wasu masu fada aji daga yankin na Arewa maso yamma a yayin ziyarar jaje ga gwamnan Legas

Legas - Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da takwaransa na jihar Kano Abdullahi Ganduje da wasu manyan baki daga Arewa a jiya sun ziyarci wurin da ginin bene mai hawa 21 ya ruguje a unguwar Ikoyi da ke Legas.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya jagorance su zuwa wurin. Tawagar ta ce ta je jihar ne domin jajanta wa jama’a kan rashin da aka yi, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Gwamnonin Arewa maso yamma da tawagarsu a Legas
Gwamnoni da wasu manyan Arewa sun kai ziyarar jaje inda bene ya ruguje a Legas | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Masari ya ce:

“Muna nan muna wakiltar gwamnonin Arewa maso Yamma don jajantawa Gwamna Babajide Sanwo-Olu, iyalan wadanda suka rasu da kuma ‘yan Legas kan wannan mummunan lamari.
“Ba za mu iya tserewa manyan gine-gine a Legas ba, amma dole ne mu tabbatar da cewa ba sa jawo asarar rayuka da dukiyoyi. Mun ji dadin yadda gwamnan ya kafa kwamitin bincike da za ta bankado abin da ya faru a nan.
“Ba abin da za mu iya sai dai mu sake jajanta wa gwamnan da al’ummar Jihar Legas game da faruwar lamarin, kuma mu yi addu’a ga Allah kada hakan ya sake faruwa. A madadin al’ummar Arewa maso Yamma, ku karbi ta’aziyyarmu da jaje.”

Leadership ta rahoto cewa, shima da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Ganduje ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici amma ya yabawa gwamnan da ya dauki matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

Rigima ta nemi ta kaure a taron Gwamnonin APC, sai da Shugaban Gwamnoni ya tsoma baki

A cewarsa:

"Lagos babban birni ne. Sannan kuma kwatanta shi da duk wani babban birni a duniya, da kuma la’akari da irin abubuwan da ya kebantu da shi na rashin wadataccen fili don habaka shi, da yawan jama’a, da gina manyan gine-ginen da ba za a iya kauce masa ba. Amma abin takaici ne yadda muka tsinci kanmu a cikin wannan hali.”

Sanwo-Olu ya godewa takwarorinsa da suka kai masa ziyara tare da yaba musu bisa wannan karimcin. Ya kara da cewa matakin nasu ya nuna cewa ba Legas ba ita kadai bace tana da 'yan uwa.

Gwamnan Legas ya je wurin da bene ya ruguje domin ganewa idonsa abin da ya faru

A rahoton mu na baya, jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya isa wurin da ginin bene mai hawa 22 a Ikoyi ya ruguje.

Rahotanni sun nuna cewa Sanwo-Olu ya ziyarci wurin da lamarin ya faru a yau da misalin karfe 1 na rana.

Kara karanta wannan

Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Gwamnan APC ga Buhari

Kafin isowar gwamnan, an fitar da wasu gawarwaki biyu daga baraguzan ginin da ya ruguje, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 22, PM News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.