Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da dimbin matafiya a hanyar Kaduna/Abuja

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da dimbin matafiya a hanyar Kaduna/Abuja

Tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da dimbin matafiya daga cikin motocinsu a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da yammaci Lahadi, 21 ga Nuwamba, 2021.

Har yanzu ba'a san adadin wadanda aka sace ba.

Wani faifan bidiyo da aka saki a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya nuna motoci akalla biyu da aka kwashe wadanda ke ciki tsakiyar titi.

A bidiyon na sakwanni 31, an ji mai daukan bidiyon yana cewa:

"Wayyo Allah, sun kwashe abokanmu, yanzu muke zuwa daga Kaduna. Yau 21 ga Nuwamba 2021."

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da dimbin matafiya a hanyar Kaduna/Abuja
Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da dimbin matafiya a hanyar Kaduna/Abuja Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A riwayar Daily Nigerian, yan bindigan sun budewa matafiyan wuta ne misalin karfe 4 na yamma.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Majiyar ta ce wanda suka yi kokarin guduwa an harbesu yayinda wadanda suka tsaya aka shiga da su cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng