Rikicin VAT: Kano kadai ta tara harajin VAT da ya fi na yankin kudu maso gabas a 2021

Rikicin VAT: Kano kadai ta tara harajin VAT da ya fi na yankin kudu maso gabas a 2021

  • Bincike ya bayyana adadin kudaden da gwamnatin tarayya ta tara a karkashin shirin karbar harajin VAT daga jihohi
  • A bangaren Arewa, jihar Kano ta tara maso mafi tsoka, wanda ya haura na jumillar jihohin kudu maso gabas gaba daya
  • A rahoton da muka samo, mun tattaro muku kadan daga cikin kididdigar da ke cikin takardar jumillar harajin na VAT a 2021

Nigeria - Jihar Kano ta lallasa jihohin Kudu Maso Gabashin Najeriya guda biyar gaba dayansu wajen tara harajin VAT na watanni takwas na farkon shekarar nan ta 2021.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan cece-kucen da ake yi kan batun VAT, batutuwan da suka shafi shari'a da kuma tattaunawar siyasa tsakanin gwamnatin tarayya da wasu jihohi, musamman daga kudu.

VAT: Kano kadai ta tara harajin da ya fi na yankin kudu maso gabas a 2021
Kididdigar harajin VAT na watanni 8 a 2021 | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Wani rahoto na musamman da Daily Trust ta samu ya nuna cewa, bayanan da aka samu na VAT daga Hukumar tara haraji ta FIRS, sun nuna cewa Kano ta tara N24.4b, fiye da kudaden da jihohi biyar suka tara na N20bn.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja

Bayanai sun nuna cewa jihar Kaduna da ta samu N19bn ita ma ta fi Akwa Ibom (N9.3bn), Bayelsa (N13bn), Delta (N13bn), Edo (N9bn), da Ogun (N11bn).

Misali, N19.8bn na Kaduna ya fi na Abia, Cross River, Osun, Ekiti, Ondo da kuma Imo.

Abia, bisa ga kididdigar, ta tara N2.2bn wanda ke wakiltar 0.22%; Kuros Riba ta tara N1.9bn, 0.19%; Osun ta tara N2.07bn, 0.20%; Ekiti ta tara N6.2bn, 0.62%; Ondo ta tara N4.8bn, 0.48%, yayin da Imo kuma ta tara 1.01bn wanda ke wakiltar 0.10 %.

Yobe a Arewa maso Gabas ta tara N9.3bn mai gogayya da Akwa Ibom (N9.3bn) kuma sama da Edo (N9bn), Ebonyi (N7.2bn) da Ekiti (N6.2bn).

Legas da babban birnin tarayya, sun ba da 65.22% na jimillar VAT, yayin da sauran jihohi 35 suka ba da 34.78% a watannin.

Alkaluman sun nuna cewa Legas ce ke kan gaba da 41.5% na adadin harajin VAT wanda ya kai N421.2bn yayin da Zamfara ta samu mafi karancin kaso, N762.5m wato 0.08% bisa dari na jimillar kudaden.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Babban birnin tarayya ne ke biye da Legas wanda ya tara N241bn ko kuma 23.74 %; Rivers ta tara N92.3bn, 9.09 % yayin da Oyo ke biye da N61bn wanda ke wakiltar 6.01%, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnonin Arewa 5 da na Kudu 5 da suka fi amfana da harajin VAT a Najeriya

A baya mun kawo muku rahoto cewa, jihohin Arewacin Najeriya biyar da wasu biyar daga kudancin Najeriya sun karbi N373.84bn daga cikin N836.51bn da aka samu daga VAT.

Jaridar Punch tace wadannan jihohi goma sun karbi wadannan kudi ne a cikin watanni 14.

Binciken da hukumar tattara alkaluma na kasa watau NBS ta fitar a game da kason FAAC ya bayyana abin da aka ba jihohi tsakanin farkon 2020 da 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.