Nasarawa: 'Yan sanda sun bankado yunkurin sace jigon PDP

Nasarawa: 'Yan sanda sun bankado yunkurin sace jigon PDP

  • Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da dakile yunkurin garkuwa da Umar Nasiru Black, jigon jam'iyyar PDP a jihar
  • Kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya sanar, sun samu kiran gaggawa inda a take jami'ai suka dira gidan dan siyasan
  • Kafin 'yan bindigan su ranta a na kare, sun buga wa Umar Nasiru Black sanda a goshi tare da harbin makwabcinsa a kafa

Nasarawa - Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta bankado yunkurin sace wani Umar Nasiru-Black, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na yankin Nasarawa ta kudu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ramhan Nanseli, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a garin Lafia.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

Nasarawa: 'Yan sanda sun bankado yunkurin sace jigon PDP
Nasarawa: 'Yan sanda sun bankado yunkurin sace jigon PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
Ya ce, "A ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba wurin karfe takwas na dare, mun samu kira kan cewa 'yan bindiga shida sun kutsa gidan shugaban PDP wanda ke yankin Bukan Kwato da ke Lafia kuma sun yi yunkurin garkuwa da shi.
"Bayan samun wannan bayani, kwamishinan 'yan sandan jihar, Adesina Soyemi, ya gaggauta aika kungiyar sintiri ta 'yan sanda da ke yankin zuwa gidan tare da bankado kokarin garkuwa da shi."

Daily Trust ta ruwaito cewa, a kokarin tserewa, miyagun sun buga wa Umar Nasiru Black sanda a goshinsa kuma sun harbi daya daga cikin makwabcinsa a kafa kafin ya tsere.

A halin yanzu ana kokarin damke 'yan ta'addan da suka yi aika-aikar.

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

A wani labari na daban, a ranar Alhamis hankula sun matukar tashi bayan an tsinta gawar limamin makabartar Kubwa mai suna Malam Abdurrashid Usman a gona inda ya je samo wa iyalinsa itace. Wani dan uwan mamacin mai suna Adamu Sama'ila, ya ce limamin ya bar gida wurin karfe goma na safe amma bai dawo ba, Daily Trust ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

SSGn Niger ya bayyana yankuna 5 da Boko Haram ke rike da su a jihar

Ya ce, "Matarsa ta fita domin ba ta gida a lokacin. Ta fita saide-saide. Ta gane cewa ba ya nan ne wurin karfe shida lokacin da ta dawo ba ta tarar da shi ba. Hakan yasa ta yi magana.
"Mun shiga daji wurin gonar Gado-Nasko daga karfe takwas har zuwa 12 na dare amma ba mu gan shi ba. Mun dai samu kayanshi, amalanken da yayi amfani da ita, gatarinsa da itace."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng