Uba ya siyar da jaririnsa kan N350,000, ya yiwa mahaifiyar yaron karyar cewa ya mutu

Uba ya siyar da jaririnsa kan N350,000, ya yiwa mahaifiyar yaron karyar cewa ya mutu

  • Jami'an 'yan sanda a jihar Abia sun yi ram da wani mutum, Appolos Ndubuisi, bisa zargin siyar da dansa namiji kan N350,000
  • Ndubuisi ya yiwa mahaifiyar dan karyar cewa ya mutu a wajen haihuwa
  • Sai dai asiri ya tonu a lokacin da ta dauki cikin 'da na biyu inda ya ce lallai zai ta koma wajen da ta haifi na farkon

Jihar Abia - Rundunar 'yan sanda a jihar Abia, ta kama wani dan shekara 40, Appolos Ndubuisi, bisa zargin siyar da dansa namiji kan N350,000, bayan ya yaudari mahaifiyarsa da cewar ya mutu a lokacin haihuwa.

An tattaro cewa Ndubuisi ya hada kai da wata Rose Godwin Chinweikpe, wacce ke da wajen karbar haihuwa a garin Owoahia-Afor da ke yankin Obingwa, wajen siyar da jinjirin.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa

Uba ya siyar da jaririnsa kan N350,000, ya yiwa mahaifiyar yaron karyar cewa ya mutu
Uba ya siyar da jaririnsa kan N350,000, ya yiwa mahaifiyar yaron karyar cewa ya mutu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa matar Ndubuisi, Deborah Onukaogu ce ta haifi jinjirin wanda ya kasance bakwaini.

Da take jawabi ga manema labarai a Umuahia, kwamishinar 'yan sandan jihar Abia, Misis Janet Agbede, ta ce Omukaogu ta dauki cikin Appolos Ndubuisi, dan asalin kauyen Umuariaga a yankin Ikwuano da ke jihar.

Kwamishinar ta bayyana cewa Onukaogu ta sanar da 'yan sanda cewa Ndubuisi bai cike sharudan da zai sa ta zamo matarsa ta sunna ba.

Sai dai kuma, an tattaro cewa Onukaogu ta haifi da namiji a ranar 26 ga watan Yunin 2021 amma wadanda ake zargin, Ndubuisi da Rose suka hada kai tare da ikirarin cewa yaron bakwaini ne.

Jaridar ta kuma tattaro cewa Deborah ta sake daukar Ndubuisi wanda ya nemi ta sake zuwa asibitin Rose don sake haihuwa a wajen.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Edo Volunteers for Tinubu 2023' tana goyon bayan ƙusan APC a zaben 2023

Sakamakon zargi da take game da bakwainin da aka ce ta haifa, sai Deborah ta shigar da kara ofishin yan sanda wanda ya yi sanadiyar kama mutanen biyu.

"Mai kara, Misis Deborah Onukaogu ta amince da labarin cewa danta bakwaini ne da zuciya daya sannan ta sake daukar wani cikin. Ndubuisi ya bayar da shawarar cewa ta sake komawa asibitin da ta haifi bakwainin.
"Sai Deborah ta ki amincewa da shawarar amma sai mai shirin zama mijin nata, Appolos Ndubuisi, yace lallai sai ta je sannan ya fada mata cewa za su siyar da jinjirin da take dauke da shi idan ta haihu. Sai ta shigar da kara ofishin yan sanda.
"Bincike ya nuna cewa bakwainin da aka ce ta haifa karya ne. Mai karar ta haifi danta namiji a ranar 26 ga watan Yunin 2021 amma sai wadanda ake zargin suka hada kai suka siyar da jinjirin kan N350,000.

Kara karanta wannan

Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq

"Bincike ya kuma nuna cewa Ndubuisi ya dauki N300,000 yayin da Rose Godwin ta dauki sauran N50.000 na karbar haihuwa da tayi."

A wani labari na daban, wani abun bakin ciki ya afku a jihar Jigawa a daren ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba, lokacin da wani jirgin ruwa ya nitse, inda wasu 'yan mata bakwai suka rasa ransu.

A bisa ga rahoton sashin Hausa na BBC, lamarin ya afku ne a lokacin da 'yan matan ke kokarin tsallake wani kogi a hanyarsu ta dawowa daga taron Maulidi da aka yi a garin Gasanya.

An tattaro cewa jirgin na dauke da mutane 12 ne lokacin da ya kife a tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa, inda bakwai suka rasu, sauran biyar din kuma suka tsallake rijiya da baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng