‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Prince Eze Madumere
  • Lamarin ya afku ne a karamar hukumar Mbaitoli a safiyar ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba
  • Maharan sun yi ta harbi ba kakkautawa kafin suka yi awon gaba da dattijon mai shekaru 89

Jihar Imo - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Prince Eze Madumere, a garin Iho da ke karamar hukumar Ikeduru na jihar.

An tattaro cewa maharan sun yi awon gaba da basaraken mai shekaru 89 a karamar hukumar Mbaitoli a safiyar ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo Hoto: Prince Eze Madumere
Asali: Facebook

An kuma rahoto cewa maharan sun yi ta harbi ba kakkautawa domin tsoratar da mutane kafin suka yi awon gaba da shi, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 7 kisar gilla a Tor-Togan

Prince Eze Madumere ya tabbatar da lamarin ga Channels TV sannan ya bayyana cewa wadanda suka sace mahaifin nasa sun kira iyalin.

A halin da ake ciki, an ce tuni rundunar yan sandan jihar suka fara aiki domin kama wadanda ake zargin.

'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

A wani labarin, mun ji cewa yayin da ‘yan bindiga su ka kai farmaki garin Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja, sun halaka mafarauci sannan suka yi garkuwa da fiye da mutane 30.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da aukuwar lamarin, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, lamarin ya auku da misalin 2am na Laraba inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun bi sawun ‘yan bindigan don ceto wadanda su ka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng