NAHCON: Adadin gurbin da muke sa ran Saudiyya zata baiwa Najeriya a Hajjin bana
- Da yake tabbatar da gudanar da aikin Hajjin bana, wani jigo a hukumar NAHCON ya bayyana adadin da ake sa ran za su yi aikin Hajji bana
- Jami'in ya ce ana sa ran akalla mutane sama da duba 40 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga Najeriya
- Ya bayyana haka ne yayin wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa, inda ya bayyana yaddda tsarin Hajjin bana yake
Abuja - Yayin da duniya ta samu saukin annobar Korona, kasar Saudiyya kuma ta cire duk wani takunkumi a Harami, Najeriya na ci gaba da shirin tunkarar aikin Hajjin bana.
A Hajjin bana, Najeriya na sa ran samun izini daga kasar Saudiyya na tura mahajja sama da 47,500.
Sabanin shekarun baya da Najeriya ke samun adadin mahajjata da suka kai akalla 95,000, a wannan shekarar Najeriya na sa ran Saudiyya ta ba da 50% na adadin mahajjata da aka saba.
Hasashen adadin na fitowa ne daga bakin kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga da yada labarai na hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Momoh a yayin wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa.
Ya yi bayanin, duk da cewa rashin samun damar yin aikin Hajji a shekarun 2020 da 2021 na iya jawo karin maniyyata aikin Hajjin, ya ce Saudiyya ba lallai da ta ba da gurbi mai yawa ba saboda dalilai na tsaron lafiya.
Da wakilin namu ya tambaye shi adadin da ake sa ran Najeriya za ta tura, Prince Momoh ya bayyana cewa:
"Muna fatan Najeriya kasancewar babbar mai ruwa da tsaki a aikin Hajji, za su yi la’akari da mu su ga ko za mu iya samun kashi 50% din 95,000, wanda zai kai kusan 47,500."
Hajjin bana zai fi na 2020 da 2021
A cewarsa, duba da wannan ne hukumar ta ce da yiyuwar rage adadin mutanen da za su yi rajistar aikin Hajjin na bana a Najeriya duk da akwai masu bukata.
Duk da haka, ya ce abin a yaba ne kasancewar a shekarar 2020 mutane 10,000 ne kadai suka yi aikin Hajjin su ma din wanda aka kebe kuma mazauna Saudiyya, inda aka samu kari a 2021 zuwa 60,000.
Tabbas akwai aikin Hajji a shekarar 2022, Maniyyata su shirya, NAHCON
A baya mun kawo muku rahoton cewa, 'yan Najeriya zasu samu damar sauke farali a kasa mai tsarki.
NAHCON ta ce babu tantama atana da tabbacin wannan shekarar 2022, maniyyata zasu gudanar da Hajji.
Da yake fira da Legit.ng Hausa, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata dake faɗin Najeriya su fara shiri tun yanzun.
Asali: Legit.ng