Da duminsa: Shugaba Buhari ya amince da kafa sabuwar jami'ar tarayya a wata jihar arewa

Da duminsa: Shugaba Buhari ya amince da kafa sabuwar jami'ar tarayya a wata jihar arewa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa sabuwar jami’ar kimiyar lafiya ta tarayya a jihar Benue
  • Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, ya ce Buhari ya amince da sabuwar jami'ar ne a zaman majalisar zartarwa a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba
  • Hakan na zuwa ne yan watanni bayan shugaban kasar ya amince da kafa sabbin jami'o'i guda biyar a Najeriya, waɗanda zasu maida hankali a ɓangaren lafiya da fasahar zamani

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, ya amince da kafa sabuwar jami’ar kimiyar lafiya ta tarayya a Otukpo, jihar Benue.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan zaman majalisar zartarwa wanda Buhari ya jagoranta, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalilin da yasa wajibi shugaba Buhari da Arewa su goyi bayan Bola Tinubu a 2023

A ruwayar Thisday, ta nakalto Adesina yana cewa:

"Kawai ina son sanar da cewa an amince da kudirin kafa Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya kuma za a bude shi a Otukpo, Jihar Benue.

Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya

A watan Yuni ne Shugban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kafa sabbin jami'o'i guda biyar a Najeriya, waɗanda zasu maida hankali a ɓangaren lafiya da fasahar zamani, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya ɗauki wannan matakin ne domin cike babban gurbin likitoci masu duba marasa lafiya, binciken lafiya da kuma samar da magunguna.

Hakazalika Buhari ya amince da fitar da biliyan N4bn na farawa ga jami'o'in fasaha da kuma biliyan N5bn ga jami'o'in kimiyyar lafiya daga asusun TETFund domin tabbatar da anfara aikin da wuri.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa da manyan gwamnati sun isa jihar Kano domin jana’izar Sani Dangode

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

A wani labarin, ministan kwadago, Chris Ngige, ya ce ma'aikatar kudi da tsare-tsare ta tarayya za ta fara rabon kudade ga jami'o'i a ranar Laraba, rahoton Premium Times.

Ministan ya ce gwamnati na da tabbacin cewa kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ba za ta tafi yajin aikin da ta shirya zuwa ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin 'Politics Today' na Channels TV a ranar Talata, 16 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng