Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal
- A makon nan ne aka samu yawaitar hare-hare a yankunan jihar Sokoto, lamarin da ya kai ga hallakar mutane da yawa
- Rahotanni sun bayyana irin barnar da 'yan bindigan suka yi, inda suka hallaka mutane sama da 50 a cikin kwanaki biyu
- A rahoton da muka samo, mun tattaro yadda gwamnati ta bayyana adadin mutanen da 'yan ta'addan suka hallaka
Sokoto - Mutum 57 ne aka kashe a cikin kwanaki biyu a jihar Sokoto yayin da ‘yan bindiga suka kai farmaki, inji rahoton Daily Trust.
Adadin wadanda suka mutu a hare-haren na ranar Lahadi da Litinin a karamar hukumar Goronyo da ke jihar ya karu zuwa 43 daga 15, yayin da wasu 14 suka mutu a ranar Talata a hare-haren da aka kai a kauyukan karamar hukumar Sabon Birni ta jihar.
Jaridar Vanguard gwamnan Aminu Tambuwal, wanda ya tabbatar da harin da aka kai kan kananan hukumomin biyu a jiharsa a jiya, ya ce hakan ya faru ne a kananan hukumomin Goronyo da Illela.
Harin na baya-bayan nan wanda aka kashe mutane 14 ya faru ne sa’o’i kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin tura karin kayan aikin soji zuwa jihar domin magance matsalar rashin tsaro.
Wani mazaunin unguwar Sabon Birni da ya tabbatar da faruwar harin, ya ce, ‘yan bindiga sun mamaye wasu kauyuka a gundumar Unguwan Lalle da daren ranar Talata.
A cewarsa, sun kashe wani mutum Abdullahi Usman a Unguwan Lalle, mutum tara a kauyen Tsangerawa, hudu a Tamindawa.
Ya kara da cewa:
“Sun kuma bude wuta kan wata mota a kauyen Gajid, inda suka kashe mutane uku ciki har da direban."
Majiyar ta ce fasinjoji biyar ne suka samu raunuka a harbin bindiga, a halin yanzu kuma suna samun kulawa a wani asibiti.
An kuma ce 'yan bindigan sun yi garkuwa da mutane uku a kauyen.
Daga baya an sako mutanen bayan yarjejeniyar da aka yi cewa mutanen yankin za su biya harajin Naira miliyan biyu nan da ‘yan kwanaki.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Kamaluddeen Okunlola ya ce maharan sun kashe mutane takwas.
A hirarsa da Daily Trust, Kwamishinan ya ce:
“Sun kai hari a wasu kauyuka masu nisa da ba a iya isa saboda rashin hanya. Amma da yardar Allah za mu same su. Muna bibiyarsu”.
An tattaro cewa a wani samame da aka kai da daren Lahadi zuwa wayewar garin ranar Litinin, an kashe mutane 13 a garin Illela da ke kan iyaka da jamhuriyar Nijar sannan an kashe mutum biyu a Goronyo mai tazarar kilomita 76; gabas da Sokoto.
Sai dai adadin ya karu zuwa 43 a jiya lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi bayani a ziyarar ta'aziyyar da ya kai Illela.
A baya dai Gwamna Tambuwal ya bayyana maharan a matsayin 'yan bindigan a matsayin 'yan ta'adda, yayin da shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da harin, ya kuma ce sojoji suyi amfani da na’urori na zamani domin zakulo maharan.
A cikin wata sanarwa a ranar Laraba mai dauke da sa hannun mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Muhammad Bello, Tambuwal a ziyarar da ya kai garin Illela ya bayyana hare-haren a matsayin abin tayar da hankali.
Ya ce:
"Wannan ba karamin abu ba ne... Wannan lamarin ya taba mu sosai."
Sai dai ya yabawa hukumomin kananan hukumomi da sarakuna da shugabannin al’umma bisa yadda suka shirya jami'an sa kai da ke aiki tare da jami’an tsaro a yankin bisa doka.
Ya roke su da kada su karaya da harin na baya-bayan nan. ya ce, ya kamata hakan zaburar da su domin su rubanya kokarinsu.
Gwamnan ya ba su tabbacin taimakon gwamnati a duk lokacin da ake bukata, yayin da yake addu'ar Allah ya jikan wadanda suka mutu.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin dakatar da harkokin sadarwa a sassan jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina da Kaduna, domin mayar da martani ga ‘yan fashi da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.
Sai dai wasu masana na yin kira da a sauya salo domin masu aikata laifuka suna tafka laifukan da suka hada da garkuwa da mutane da kuma yi wa mata da yara fyade a daidai lokacin da mutanen yankin ke fama da wahalar damar kiran waya don neman tallafi.
'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje
A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu da ake zargin 'yan awaren Ambazonia ne daga kasar Kamaru sun yi barna a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba.
A cewar mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, wadanda ake zargin sun bindige hakimin kauye da wasu mazauna unguwar Manga.
Kauyen Manga yana da tazarar kilomita 20 daga Dam din Kashimbilla.
Asali: Legit.ng