Hakimin Kiyawa ya soki tsarin ba iyaye toshiyar baki domin su amince da karbar riga-kafi a arewa
- Hakimin Kiyawa, Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa, ya magantu kan abun da ke ci masa tuwo a kwarya a yankin arewacin kasar
- Kiyawa ya soki tsarin bai wa iyaye a arewa toshiyar baki da sunan kyauta domin su yarda da karbar riga-kafi don tsaron lafiyar 'ya'yansu.
- A cewarsa wannan toshiyar baki da ake basu yasa suna ganin lamarin lafiyar 'ya'yansu ya fi muhimmanci ga gwamnati fiye da su a matsayinsu na iyaye
Jihar Jigawa - Wani jagora kuma mai fafutuka a kan harkar kula da lafiyar mata masu juna biyu da masu jego a jihar Jigawa, Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa, ya yi tsokaci kan wasu matsaloli da ke addabar arewa.
Kiyawa ya yi watsi da tsarin na bai wa iyaye kyaututtuka a matsayin toshiyar baki domin su yarda da karbar riga-kafi ga yara a yankin arewacin kasar, rahoton Daily Trust.
Ya ce matakin da gwamnati ta dauka na bayar da kyaututtuka don kawai su yarda da kula da lafiyar 'ya'yansu yasa suna ganin lamarin ya fi muhimmanci ga gwamnati ba wai a gare su iyaye ba.
Aliyu, wanda ya kasance Hakimin Kiyawa kuma mamba a kwamitin a kwamitin bayar da riga-kafi na yau da kullun na karamar hukumar Kiyawa, ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da aka gudanar a fadarsa.
An shirya taron ne a wani bangare na bikin ranar cutar huhu ta duniya ta 2021 da kungiyar SCI ta shirya.
Kiyawa ya yi sharhi ne kan rahotannin da ke nuna an samu raguwar mace-macen yara kanana masu fama da cutar huhu daga kashi 12.3 cikin 100 zuwa kashi 3.9 cikin 100 a jihar Jigawa.
Hakimin wanda ya kuma kasance tsohon kwamishina a jihar Jigawa ya ce:
"Wannan matakin da gwamnati ta dauka ya sanya jama'a da iyaye suna gani cewa lafiyar 'ya'yansu yana da muhimmanci ga gwamnati ba wai gare su ba a matsayinsu na iyaye."
Rahoton ya kuma kawo cewa jagoran cibiyar lafiya a karamar hukumar Kiyawa, Malam Musa Muhammadu, ya ce cutar huhu ta ragu matuka a karamar hukumar, sakamakon sa hannun kungiyar SCI.
Har ila yau, ya ce billo da shirin INSPIRING da kamfanin GlaxoSmithKline (GSK) ya dauki nauyi tare da tallafawa ma’aikata da cibiyoyin kiwon lafiya a yankin da kayan aikin jinya na sama da naira miliyan 50 sun taimaka wajen cimma wannan nasara.
A wani labari na daban, tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, Farfesa Attahiru Jega, yace shugabannin Najeriya ba su da ilimin kasancewa a matakin da suke sam.
Da yake jawabi a wurin lakcar Maitama Sule, wanda kungiyar ɗaliban Arewa SW-CNG ta shirya a Katsina, ranar Litinin, tsohon shugaban INEC ɗin ya alaƙanta matsalolin Najeriya da rashin jagoranci mai kyau.
Bidiyon yadda iyayen matashi suka nuna farin ciki mara misali yayin da ya duba sakamakon jarrabawar zama lauya
A rahoton Dailytrust, Jega yace Najeriya ba ta yi dacen shugabanni ba idan ana magana kan gudanar da ayyukan cigaban ƙasa.
Asali: Legit.ng