Rikicin APC: 'Yan sanda sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a Abuja

Rikicin APC: 'Yan sanda sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a Abuja

  • Jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja a yau Laraba
  • Rahotanni sun bayyana cewa, an ga jami'an 'yan sanda da na DSS jibge a hanyoyin shiga da fita a sakateriyar
  • An ce ana tunanin barkewar wata zanga-zanga ne daga wasu 'yan jam'iyyar APC da ke adawa da gwamna Buni

Abuja - Adadi mai yawa na 'yan sanda cikin manyan motocin sintiri hudu ne suka mamaye hanyar shiga da fita a titin Blantyre da ke cikin sakatariyar jam’iyyar APC a Abuja.

An tattaro a ranar Laraba cewa ‘yan sandan da jami'an tsaro na DSS suna wurin ne domin dakile yiwuwar tabarbarewar doka da oda.

Yanzu-Yanzu: 'Yan sanda sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a Abuja
Taswirar babban birnin tarayya Abuja | Hoto: wikipedia.org
Asali: UGC

Wakilin jaridar Punch ya samu labarin cewa jami’an tsaron sun taru ne bayan samun rahotannin tsaro game da shirin zanga-zangar da 'yan APC suka shirya yi na nuna adawa da yadda jam’iyyar ta gudanar da zabuka a taronta na gangami na jihohi.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

Daily Trust ta ce wasu ‘ya’yan jam’iyyar sun shirya gudanar da zanga-zangar adawa da Gwamna Mai Mala ne kan ci gaba da jagoranci kwamitin riko/tsare-tsare na musamman.

Da yake tsokaci kan lamarin, sakataren kwamitin rikon, Sen John Akpanudoedehe, ya shaidawa manema labarai cewa jami’an tsaro sun mamaye wurin ne bayan samun rahoton tsaro.

A cewarsa:

“Babu wani abu da ke faruwa. Sun sha zuwa wurin a duk lokacin da muke bukatar kiyaye Sakatariyar.”
“Ba ku da ikon karanta rahotannin tsaro, don haka ba za ku iya tambayata akai ba. Idan wani abu ya faru a yanzu, za su fadi me suke yi. Akwai abubuwa da yawa da suka shafi tsaro da ba ku sani ba.
“Abu ne na yau da kullum. 'Yan sanda suna hulda da Ministan FCT, IG da sauran mutane idan suna da wani bayani. Ba a nan kadai ba, idan za ku je Abuja, za ku je filin jirgin sama, mu ma muna da hakkin kare masu aiki a nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki Birtaniya, Faransa da Afrika ta kudu

“Mun karanta rahotannin tsaro kuma na tabbata kun san cewa muna da kowace irin hukumar tsaro a sakateriyar mu. Muna aiki ne kawai da rahotannin tsaro, babu wani abin fargaba."

APC ta yi waje da jigonta saboda ya taya APGA murnar lashe zabe a Anambra

A wani labarin, jam’iyyar APC reshen jihar Anambra ta kori sakataren yada labaranta Okelo Madukaife saboda taya zababben gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo murnar lashe zabe.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Basil Ejidike ne ya sanar da korar Madukaife a wani taron manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambra a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba.

Ya ce Madukaife da aka dakatar a watan Yunin wannan shekara ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin sakataren yada labaran APC har ya zuwa yanzu, ya kuma bayyana a gidan talabijin na kasa don taya Soludo na jam’iyyar APGA murnar lashe zabe.

Kara karanta wannan

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.