Wata sabuwa: Kamfanin Coca-Cola ya maka kamfanin Pop Cola a kotu saboda satar fasaha
- Kamfanin Coca-Cola ya maka wadanda ke samar da abin sha na Pop Cola a gaban kotu bisa laifin satar fasaharsu ta kasuwanci
- Coca-Cola ta ce, Pop Cola ya saci tambarin da Coca-Cola ya yiwa rajistar kasuwanci ba a Najeriya kadai ba, a duniya baki daya
- An saurari batun a babban kotun tarayya da ke Kano, inda aka dage karar zuwa wani lokaci don wanda ake kara ya kara shirya wa
Kano - Kamfanin Coca-Cola ya maka kamfanin Mamuda Beverages Nigeria Limited, masu sayar da kayan zaki na Pop-Cola, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kano kan satar tambarin kasuwanci, Daily Nigerian ta ruwaito.
An kaddamar da Pop-Cola ne a cikin watan Yunin wannan shekara, inda Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana a matsayin babban mai tallata hajar.
Wani kwafin karar da kafar yanar gizo ta Kano Focus ya samu, ya nuna cewa Coca-cola na zargin kamfanin Mamuda Beverages da amfani da tambarin kasuwanci mai suna 'RIBBON Device' a jikin Pop Cola, wanda kwaikwayon inji Coca Cola na haifar da rudani a tambarin kasuwancinta.
A cewar kudurin, wanda ake kara (Mamuda Beverages Nigeria Limited) yana rabawa tare da tallata kayayyakinsa na Pop-Cola a kasuwa wanda ya kunshi dukkan abubuwan da suke tattare da shahararriyar rigar cinikin Coca-cola.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar rahoton, Coca-Cola ta yi ikirarin cewa ita ce ta mallaki tambarin 'coca-cola (a rubuce)' da kuma 'dynamic ribbon device' a Najeriya da ma duniya baki daya, inda ya kara da cewa kamfanin ya yi rajista da kasashen duniya ciki har da Najeriya.
Don haka Coca-Cola na neman a hana Pop-Cola, ma'aikata ko wakilai daga yin amfani da, saka ta ko nuna samfurinta da dai sauran bukatu da suka shafi daukar matakin doka.
Sai dai kuma a ranar Talatar da ta gabata ne aka nemi lauyan Coca-Cola da ke kan karar ya shigar da karin takardun shaida da karin wasu takardu.
Lauyan wanda ake kara, George Ogunyomi, ya bukaci kotun da ta tabbatar da cewa ba zai kasance kawai a ci gaba da shari’ar ba ba tare da ba da lokaci ga wanda ake kara ya amsa wannan karin bukatu da mai kara ya shigar ba.
Alkalin kotun Muhammad Nasir-Yunusa ya dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Disamba domin ci gaba da sauraren karar.
Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta saka sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa
A wani labarin, Kungiyar masu samar da ruwan sha ta Najeriya (WAPAN) ta bayyana cewa farashin ruwan ‘pure water’ na iya tashi daga N20 a yanzu zuwa N50 kan idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin haraji kan abubuwan shaye-shaye na yau da kullum.
Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson ne ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar a Legas. 'Yan Najeriya sun shaidi tashin farashin ruwa sau uku a cikin shekarar 2021; daga N5 zuwa N10 da kuma N20.
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kudi a watan Agusta 2021, ya yanke shawarar cewa za ta yi wa dokar Kudi kwaskwarima don dawo da haraji kan duk wani abin sha na yau da kullum.
Asali: Legit.ng