Bai kamata yan bindiga sun yi tunanin banza suke ci ba, Shugaba Buhari
- Shugaba Buhari ya yi kakkausan gargaɗi kan yan bindiga bayan kashe mutum 15 a kananan hukumomin jihar Sokoto
- Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba zata bar wasu tsiraru su hana yan Najeriya zaman lafiya ba
- Yace gwamnatinsa zata cigaba da samar wa jami'an soji kayan aiki domin su kawo karshen waɗan nan tsagerun baki ɗaya
South Africa - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gargaɗi yan bindiga kada su yi tunanin banza suke ci, ba za'a kawar da su, kamar yadda Punch ta rahoto.
Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa ba zata bari yan Najeriya su cigaba da fama da ƙalubale kala daban-daban daga yan bindigan ba.
Buhari ya yi wannan furucin ne tun daga South Africa, yayin da yake Allah wadai da kisan mutum 15 da yan bindiga suka yi a Goronyo da Illela, jihar Sokoto.
Babban mai taimakawa shugaban ƙasa ta bangaren yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar mai taken, "Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutum 15 a Sokoto."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Buhari yace:
"Wannan rashin imanin da ake wa mutanen da basu ji ba ba su gani ba ya isa haka, ba zamu barshi ya tafi salin alin ba."
"Ina mai ƙara tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatin mu ba zata barsu haka nan ba, su cigaba da fama da matsalolin yan bindigan daji."
Wane mataki gwamnati take ɗauka?
Shugaban kasa ya kara da cewa gwamnatinsa zata cigaba da siyan makamai da kayan aikin jami'an tsaro domin tallafa musu wajen magance matsalar yan bindiga.
"Sojojin mu zasu cigaba da amfani da fasahar zamani wajen gano maboya da kuma ragaragazan yan ta'adda da makiyan zaman lafiya."
Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata
"Gwamnatin mu ba zata lamurci irin haka ba, wasu tsageru su rika fatattakar mutane daga rayuwarsu ta yau da kullum, su koma barace-barace da gudun hijira."
"Yan ta'adda ba zasu cigaba da samun sa'a ba kullum, duk daren dadewa gaskiya zata yi halinta akan karya."
A wani labarin kuma Gwamna ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace basu kaunar kawo karshen matsalar tsaro
Gwamna Bala Abdulkadir Muhammed na jihar Bauchi, yace gwamnatin Najeriya zata iya kawo karshen matsalar tsaro idan ta so.
A cewarsa matukar gwamnati zata iya datse dukkan hanyoyin sadarwa a wurraren da lamarin ya yi kamari, to komai mai sauki ne.
Asali: Legit.ng