Lamari ya yi zafi, dattawan Arewa sun zauna don neman mafita ga matsalolin Arewa
- Wata kungiyar 'yan Arewa ta gana da mambobinta domin neman mafita ga matsalolin Najeriya musannan Arewa
- Kungiyar ta koka kan yadda aka mayar da Arewa koma baya, ta hanyoyin da a da take dasu cikin aminci
- Hakazalika, mambobin kungiyar sun bayyana bukatar tashi tsaye domin kawo mafita ga matsalolin Najeriya
Kano - Kungiyar farfado da martabar Arewa (NRO) a ranar Lahadi ta tattaro masu ruwa da tsaki da dattawan yankin Arewa domin tattauna kalubalen yankin Arewa a jihar Kano.
Taron yana daga cikin kokarin suke yi na magance matsalolin da ke kara ta'azzara a yankin da yanzu haka ke karuwa cikin wani yanayi mai ban tsoro, Daily Trust ta ruwaito.
Yana daga cikin aikin kungiyar na maido da jituwa, dauwamammen zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da maido da halayya da mutunci ga mutumci da asalin Arewa.
Da yake jawabi, Shugaban kungiyar ta NRO, Gidado Mukhtar, ya koka da yadda shugabanci ke rasa ingancinsa, manufa da kuma tasirinsa, ya kara da cewa akwai bukatar a kawo gyara cikin gaggawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake karin haske a taron, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce kasancewar yankin Arewa yana da harsuna kusan 320, ba za a iya hade shi ba sai dai idan mutum ya san mene ne yankin duk da bambancin addini da banbance-banbancensa.
Shi ma da yake nasa jawabin, Bashir Tofa, ya jaddada bukatar Arewa ta tashi tsaye domin yin magana da murya daya, inda ya bayyana kasala, hassada, kiyayya, rashin aikin yi da rashin aiwatar da manufofi a matsayin muhimman batutuwan da ke haifar da barazana.
A cewarsa:
“Mun zabi shugabanni su yi mana aiki amma sun koma bautar da mu. Muna da dubban abubuwan da ba mu san yadda za mu magance su ba.
“Ba mu da hadin kai, ba ma kaunar junanmu. Me zai faru idan babu Najeriya?"
Wani dattijon Arewa, Musa Magami, ya yi kira ga kowa da kowa da su hada kai, yana mai cewa an mayar da masana’antun Arewa zuwa mafi kaskanci saboda rashin kulawa da aka yi shekaru da yawa.
Ya kara da cewa Saudiyya ta taba shiga cikin wannan hali kuma a yau ta hanyar daukar matakan da suka dace suna daya daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya.
Kungiyar ta NRO tana da mambobi sama da 600 da ke da tushe a Kano kuma tana da alaka da wasu kungiyoyi 15 wadanda na agaji ne.
Ana ci gaba da kai hare-hare Arewa
A makon nan ne aka kara samun mummunan harin 'yan ta'adda a yankin Borno, lamarin da ya kai ga mutuwar wani babban jami'in soja.
Daily Nigerian ta rahoto cewa sojojin sun kai hari kan yan ta'addan ba kakkautawa domin daukar fansa, bayan kisan da suka yi wa manyan jami'an soji.
Hakzalika, an samu jerin hare-hare a yankunan Zamfara da Katsina duk dai a cikin 'yan kwanakin nan.
'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji
A wani labarin, wasu 'yan ta'adda da ake zargin mayakan ISWAP ne a halin yanzu suna musayar wuta da sojoji a wani sansanin soja da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wasu mazauna sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogon ayarin motocin bindigu a hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.
Jama'a da dama sun tsere cikin daji yayin da wasu suka makale a gidajensu.
Asali: Legit.ng