Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki, sun halaka rayuka 9 tare da sace shanu
- A kalla mutane 9 ne su ka riga mu gidan gaskiya a kauyen Tungar Ruwa da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara
- ‘Yan bindigan ba su tsaya a nan ba, sai da su ka sace dabbobi, balle shaguna sannan su ka yi awon gaba da kayan abinci da sauran su
- Majiyoyi sun tabbatar wa manema labarai cewa lamarin ya auku ne a ranar Laraba da dare lokacin da ‘yan bindigan suka fada su na harbe-harbe
Zamfara - A kalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu a kauyen Tungar Ruwa da ke karamar hukumar Anka a jihar.
‘Yan bindiga sun fada wa kauyen inda suka sace dabbobi, balle shaguna sannan suka yi awon gaba da kayan abinci.
Majiyoyi sun tabbatar wa Channels Television yadda ‘yan bindigan suka fada garin da daren Laraba inda suka dinga harbe-harbe ko ta ina.
Sakamakon hakan ne suka halaka mutane 9 sannan wasu da dama suka ji raunuka da dama.
An samu bayanai a kan aukuwar mummunan lamarin da daren Juma’a daga bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu.
Kakakin ya bayyana yadda yanzu haka aka tura jami’an zuwa yankin don gudun kada ‘yan bindigan su kara kai farmaki, ChannelsTV ta wallafa.
Rundunar ta kara da horar da jama’a a kan bai wa jami’an tsaro hadin-kai don kawo karshen wasu miyagu da masu basu bayanan sirri.
A ranar Litinin ‘yan bindiga sun halaka ‘yan sanda 7 wuraren titin Tofa-Magami da ke karamar hukumar Gusau.
Ganau sun shaida yadda lamarin ya faru da misalin 6:00pm lokacin da ‘yan sanda suke sintiri a yankin.
Zamfara: 'Yan bindiga sun shiga gidaje suna karbar abinci, sun sheke mutum 6 tare da sace wasu
A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun halaka rayuka shida tare da sace wasu masu yawa a farmakin da suka kai kauyen Rijiya da ke karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Wani mazaunin kauyen, Mustapha Ibrahim, ya sanar da Premium Times a waya cewa 'yan bindigan sun tsinkayi yankin a tsakar ranar Lahadi.
"Sun fara harbi daga shigarsu kauyen. Ina tunanin domin su ruda mutane ne suke hakan. Sun halaka mutum shida yayin harbi. Mun kirga gawawwaki shida cif," yace.
Asali: Legit.ng