Duk da musantawar NDA, sojan da ake yada ya na da hannu a farmakin ya yi batan dabo
- Tun bayan bayyanar labarin gano sojan da ya kai farmaki NDA, har yanzu an rasa inda sojan mai mukamin sajan ya shiga
- Makarantar horar da hafsoshin soji ta NDA da ke Kaduna ta musanta labarin da ake yadawa na cewa ta cafke sojan da ya jagoranci kai farmaki a watan Augusta
- Sai dai duk da musanta hakan, har a halin yanzu babu amo balle labarin kan inda Sajan Torsabo Solomon ya shiga
An samu rudani da rashin gano takamaiman kan labarin batan wani sojan sama mai mukamin sajan mai suna Torsabo Solomon, wanda aka ce rundunar sojin ta kama shi a ranar Litinin saboda alakarsa da farmakin da aka kai NDA a watan Augusta.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a labarin da ke yawo, an ce an kama shi ne a sansaninsu da ke Yola a jihar Adamawa bayan bukatar da hukumomi daga Kaduna suka mika.
'Yan bindiga sun kai farmaki NDA a watan Augusta, sun kashe sojoji biyu tare da sace wani daya wanda daga bisani aka ceto.
Rahotanni sun cewa sajan din na aiki da makarantar sojoji da ke Yola kuma an dauke shi a jirgi zuwa Kaduna wurin karfe 8:15 na safe domin a tuhume shi kan makamai da yayi amfani da su a farmakin NDA Kaduna.
Amma a jiya, NDA ta fitar da takarda ta hannun mai magana da yawun hukumar, Manjo Bashir Jajira, ya musanta cewa Solomon na hannunsu, Daily Trust ta wallafa.
Ya bayyana cewa makarantar wuri ce ta horar da sojoji kuma ba wurin binciken tsaro bace, don haka ya shawarci jama'a da su yi watsi da duk wani bayanin karya da suka samu kuma su saurari hukumomin da ya dace domin karin bayani.
An kai hari NDA ne kawai don batawa gwamnatin Buhari suna, Mai magana da yawun shugaban kasa
A wani labari na daban, Mai magana da yawun shugaban kasa, Mr Femi Adesina, ya bayyana cewa an kai hari makarantar horon Soji NDA ne domin nuna cewa gwamnantin Buhari ta gaza. A cewarsa, yan bindiga sun shiga NDA ne don rage azamar Sojoji dake yaki da su.
Adesina ya bayyana hakan ne jawabin da ya daura kan shafinsa na Facebook ranar Alhamis. Yace dukkan masu kokarin batawa Sojojin Najeriya suna marasa godiya ne.
Yace: "Abinda ya faru a makarantar Sojoji, me manufar hakan? Abu mai sauki ne. Da gayya aka kai harin domin batawa gwamnati suna, da kuma ragewa Sojoji karfin gwiwa a daidai lokacin da suke fama da matsalar rashin tsaro."
Asali: Legit.ng