'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyukan Binnari da Jab Jab a karamar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba
  • Maharan wadanda suka kai harin daukar fansa sun kashe akalla mutane 15 ciki harda matan aure uku sannan suka kone gidaje
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da harin wanda ya afku a safiyar yau Laraba, 10 ga watan Nuwamba

Karim Lamido, jihar Taraba - Akalla mutane 15 ciki harda matan aure uku ne suka rasa ransu a kauyukan Binnari da Jab Jab a karamar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Binnari da misalin karfe 4:00 na asuba a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, inda suka dunga harbi kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba
'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba Hoto: The Guardian
Asali: UGC

An tattaro cewa mutanen kauyukan sun yi yunkurin yakar su amma sai yan bindigar wadanda yawansu ya fi 50 suka sha karfinsu.

Majiyoyi sun fada ma jaridar cewa maharan sun kai hari kauyukan guda biyu ne domin ramuwar gayya sakamakon kashe wasu masu garkuwa da mutane da yan banga suka yi a yankin yan makonni da suka gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma rahoto cewa an kashe 'yan bindiga bakwai a yayin arangamar sannan maharan da suka tsirar sun tsere da gawawwakin yan uwansu.

A yayin harin da suka kai Jab Jab, an ce yan bindigar sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje.

Mani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansu, ya yi korafi a kan rashin Jami’an tsaro.

Ya ce:

“A yanzu haka da nake magana da Ku, babu Jami’an yan sanda ko na sojoji a Binnari amma an fada mana sojoji na a hanyarsu ta zuwa yankin.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Ya kuma bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe hakimin Binnari da wasu yan banga a farkon shekarar nan.

DSP Usman Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Taraba, ya tabbatar da harin amma ya ce an tura jami’ai zuwa yankin.

Ya ce:

“A yanzu haka yan sanda na nan a kasa kuma suna kokarin dawo da zaman lafiya kuma baku da adadin mutanen da suka mutu a yanzu.”

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

A wani labarin, mun kawo cewa ana fargabar 'yan bindiga sun kashe mutane da yawa tare da kona dukiyoyinsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan wasu al'ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Harin wanda rahotanni suka ce ya fara ne da yammacin ranar Talata zuwa sanyin safiyar Laraba, yayi sanadiyyar kona gidaje da yawa da suka hada da gine-ginen gwamnati da motoci, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Shaidu sun ce akalla al’ummomi biyar ne ‘yan bindigar suka afkawa, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng