Hukumar ICPC ta bankado yadda aka aiwatar da ayyukan mazaabu sama da 300 a Jigawa da Kano
- Hukumar ICPC ta bayyana cewa ta gano yadda aka aiwatar da ayyukan mazabu 300 a jihohin Jigawa da Kano
- A cewar shugaban ICPC mai kula da jihohin, Garba Kagara, hukumarsa ta umarci yan kwangila da yan majalisu su koma su gyara
- Yace ko dai a aiwatar da aikin amma mara kyau da inganci, ko kuma a karkatar da kuɗaɗen aikin baki ɗaya
Kano - Hukumar yaƙi da ayyukan cin hanci ta ƙasa (ICPC) tace ta gudanar da bincike kan ayyukan mazaɓu 300 a jihohin Jigawa da Kano wannan shekaran.
Daily Nigerian tace kwamishinan ICPC mai kula da jihohin biyu, Ibrahim Garba-Kagara, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Kano
Yace wasu daga cikin ayyuka ba'a aiwatar da su ba kwata-kwata yayin da wasu kuma aka bubbuga su sama-sama babu inganci.
Ayyukan mazaɓu da ICPC ta gudanar da bincike a kansu, sun haɗa da gina Asibitoci, makarantu, samar da fitilun kan hanya da sauransu, a cewarsa.
A ina matsalar take?
Garba Kagara ya ƙara da cewa tuni hukumar ta umarci wasu daga cikin yan kwangila da yan majalisu su koma su gyara ayyukan da ba'a kammala ba.
Yace hukumarsa ta wayar da kan shugabannin addini, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin matasa a Jigawa kan muhimmancin san ya ido kan ayyukan da kuma kai rahoton inda akai ba dai-dai ba.
Yace a sabuwar shekara da zata shigo 2022, ICPC zata faɗaɗa wayar da kai zuwa masarautun jihar Kano guda 5.
Guardian ta rahoto Kagara yace:
"Kundin mulki ya baiwa ICPC damar bincike da gurfanar da masu aikata laifi, sannan kuma da wayar wa mutane kai su guji aikata cin hanci."
"Hukumar ta samar da wani ɓangare na yaki da cin hanci a ma'aikatu da hukumomin gwamnati domin taimaka musu, su sauke nauyin da aka ɗora musu."
A wani labarin kuma Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da mutumin gaban kotu ne bisa zarginsa da batanci ga Ganduje a shafin sadarwa na Facebook
Rahoto ya nuna cewa ana zargin mutumin da kiran gwamna Ganduje da wasu daga cikin iyalansa Barayi ba tare da hujja ba.
Asali: Legit.ng