Da Dumi-Dumi: Wuta ta barke a cikin jami'ar jihar Kaduna, ta yi mummunan barna

Da Dumi-Dumi: Wuta ta barke a cikin jami'ar jihar Kaduna, ta yi mummunan barna

  • Wata wuta da ta tashi a ƙasuwar cikin jami'ar jihar Kaduna ta kone shagunan mutane da kaya masu daraja
  • Rahoto ya nuna cewa gobarar wacce ta fara lokacin da aka dawo da hasken wutar lantarki ta yi mummunar banna ta miliyoyi
  • Wani ɗalibi ya bayyana cewa ɗalibai yan uwansa sun kira jami'an kashe wuta amma ba su zo ba

Kaduna - Wata gobara da ta tashi a kasuwar jami'ar jihar Kaduna (KASU) ta kone shaguna da dama da wasu abubuwa masu daraja, wanda akai kiyasin zasu kai na miliyoyi.

Vanguard tace duk da bayanai kan ainihin abinda ya faru ya yi wahala, amma wata majiya ta bayyana cewa wutar ta fara ne lokacin da aka kawo wutar lantarki kafin karfe 7:00 na daren Talata.

Kara karanta wannan

Namiji da raino: Wani magidanci ya lakadawa diyarsa duka har Lahira saboda ya kasa lallashinta

Ɗaliban jami'ar da dama sun nuna rashin jin daɗinsu tare da jajantawa yan kasuwan da abun ya shafa.

Gobara a KASU
Da Dumi-Dumi: Wuta ta barke a cikin jami'ar jihar Kaduna, ta yi mummunan barna Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar wasu daga cikin ɗaliban KASU, kasuwar ce kaɗai inda suke samun kayayyakin amfanin su cikin sauki da rahusa.

Shin yan kwana-kwana ba su kawo ɗauki ba?

Wani ɗalibi yace:

"Ɗalibai sun yi kokarin kashe wutan kafin zuwa jami'an kashe gobara, amma abun ya ci ƙarfinsu lokacin da wani abu ya fashe a ɗaya daga cikin shagunan dake ci da wuta."
"Wannan fashewar ne ya ƙara wa wutar karfi, har ta bazu zuwa wasu shagunan yayin da ya zama tilas ɗalibai su koma yan kallo, ba abinda zasu iya yi."
"Wutar ta fara ne lokacin da aka dawo da wutar lantarki a shago ɗaya, mun sanar da yan kwana-kwana amma ba su zo ba. Daga nan sai ɗalibai suƙa fara kokarin taimaka wa kafin wutar ta watsu."

Kara karanta wannan

Shugabannin APC na shirin tsayar da gwamnan Arewa takarar shugaban ƙasa a 2023

Ina masu shagunan?

Ɗalibin ya ƙara da cewa mafi yawan masu shagunan sun ta shi lokacin da wutar ta fara ci, domin da suna nan kila a samu saukin lamarin.

Sai dai rahoton da muka samu ya bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa kuma hukumar jami'an ta sanya jami'an tsaro a cikin lamarin.

A wani labarin kuma kun ji cewa aƙalla mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin bikin Aure

Wasu tsagerun yan bindiga sun hallaka mutum biyu yayin da suka yi kokarin garkuwa da ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Usoro Akpanusoh, a wurin bikin aure.

Honorabul Usoro Akpanusoh, ya bayyana cewa maharan shi suka so sace wa amma ya samu nasarar tserewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel