Masu garkuwa da mutane sun kashe wani kyaftin din soji mai ritaya
- Masu garkuwa da mutane sun kashe wani kyaftin din rundunar soji mai ritaya, Godfrey Zwallmark, a jihar Ribas
- Yan sanda sun yi nasarar kama mutane uku da ke da hannu a lamarin bayan iyalin mamacin sun kai masu rahoto
- Maharan dai sun nemi iyalan su biya naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa kafin suka kashe shi
Ribas - Tsagerun ‘yan bindiga sun halaka wani kyaftin din rundunar soji mai ritaya, Godfrey Zwallmark, a jihar Ribas.
Maharan sun yi garkuwa da marigayin ne a karamar hukumar Eleme da ke yankin Ribas sannan suka kashe shi, amma sai suka bukaci iyalinsa su biya naira miliyan 200 a matsayin kudin fansarsa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa iyalin marigayin sun kai rahoton lamarin ga ofishin yan sanda daga baya, inda hakan ya kai ga kama mutum uku.
Da yake zantawa da manema labarai a wajen da aka gano gawar tsohon sojan mai shekaru 64, kwamishinan yan sandan jihar Ribas, CP Eboka, ya ce lamarin ya afku ne a ranar 18 ga watan Satumban 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma ya bayyana cewa sai bayan wata daya sannan aka shigar da kara ofishin yan sanda, kamar yadda yake a ruwayar Nigerian Tribune.
Eboka ya ce suna samun rahoton lamarin sai yan sanda suka shiga aiki, inda aka yi nasarar cafke mutane uku masu suna Frank Ishie, Iwuji Reginald da Gomba Okparaji.
Ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun bukaci kudin fansa daga iyalan marigayin kafin su kashe shi.
Daya daga cikin wadanda ake zargin, Ishie, wanda ya zanta da manema labarai, ya amsa laifin.
Wanda ake zargin ya yi bayanin cewa an sace wanda lamarin ya cika da shi ne a karamar hukumar Eleme.
Ya ce an harbi mutumin ne a kafa domin ya nuna taurin kai a lokacin da suka kai shi raminsu.
Ya bayyana cewa marigayin ya zubar da jini har zuwa mutuwarsa yayin da suka ajiye gawarsa a hanyar Igbo-Etche da ke karamar hukumar Etche ta jihar.
Wadanda ake zargin sun fallasa cewa suna da hannu a garkuwa da mutane hudu sannan cewa suna boye mutanen da suka sace a mabuyarsu da ke Igbo-Etche kafin a biya kudin fansar su.
Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi
A wani labarin, mun ji cewa sabbin bayanai sun bayyana kan yadda aka halaka babban jami’in soja mai ritaya a Kaduna a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba.
Wata majiya ta kusa da iyalan marigayi AVM Mohammed Maisaka, Abubakar Gwantu ya ce kisan na iya zama abun da aka kitsa, Vanguard ta rahoto.
Rahoton ya kuma kawo cewa makwabcin nasa ya kuma bayyana cewa Maisaka ya dade baya fita saboda jinya da yake yi.
Asali: Legit.ng