Buhari ya nemi majalisa ta amince da Farfesa Omotayo a matsayin DG na NIPSS

Buhari ya nemi majalisa ta amince da Farfesa Omotayo a matsayin DG na NIPSS

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan wani farfesa a matsayin sabon shugaban hukumar NIPSS
  • Shugaban ya tura suna tare da takardun jami'in inda ya nemi majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da shi
  • Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ne ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aike wa majalisar

Abuja - The Nation ta ruwaito cewa, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da tantance Farfesa Ayo Omotayo a matsayin Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta NIPISS da ke Kuru, kusa da Jos, Jihar Filato.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar bukatar Buhari a zauren majalisar bayan dawowa daga hutun aiki na kwanaki 18 na Sanatoci domin baiwa ma’aikatun hukumomi (MDAs) kare kudirinsu na kasafin kudin 2022.

Kara karanta wannan

Kungiyar mata 'yan jarida sun koka kan tsadar rayuwa, sun mika bukatarsu ga gwamnati

Da dumi-dumi: Buhari ya nemi majalisa ta amince da Omotayo a matsayin DG na NIPSS
Majalisar Dattawan Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shugaban a cikin wasikar ya ce nadin Farfesa Omotayo a matsayin babban jami'in NIPISS ya kasance daidai da sashe na 5 (2) na dokar NIPSS ta 2004.

Wasikar mai taken “Bukatar tabbatar da nadin Farfesa Ayo C. Omotayo PhD a matsayin Darakta Janar na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta kasa (NIPSS),” tana cewa:

“Bisa tanadin sashe na 5 karamin sashe na 2 na kasa. Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun Dokar 2004, na rubuta wannan don gabatar da neman tabbatar Majalisar Dattawa, nadin Farfesa Ayo C. Omotayo a matsayin Darakta-Janar, Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru na kasa (NIPSS)."

Shugaban ya kuma mika tare da takardun karatu da gogewar aiki ta Farfesa Omotayo, kamar yadda PM News ta ruwaito wasikar na cewa:

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa Farfesa Shehu Dalhatu na Jami'ar BUK rasuwa

“CV na wanda aka zaba yana hade da wasikar. Ina fata Majalisar Dattawa za ta yi nazari tare da tabbatar da wanda aka nada ta hanyar da ta saba.”

Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba ba a Najeriya kafin ya bar ofis

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai rufe gibin kayayyakin more rayuwa a kasar kafin ya sauka a mulki, Leadership ta ruwaito.

Ya kara da cewa, sabanin gwamnatocin baya, za a yi amfani da rancen da gwamnatinsa ta karbo wajen gudanar da ayyuka domin rage yawan gibin ababen more rayuwa a kasar nan.

Shugaban ya yi magana ne ta bakin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, a wajen bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Afirka, Dokta Bamanga Tukur mai taken 'Legacies of a Legend' a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel