Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai
- Hukumar Sojin Najeriya na cigaba da samun nasara bisa yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas
- Tun bayan mutuwar Shekau, dubunnan mabiyansa sun ajiye makamansu sun fito daga cikin daji
- Daga cikinsu akwai yan matan Chibok da Daphi da aka fidda rai daga hannunsu bayan sun auri wasu cikin yan ta'addan
Borno - Tiyata Kwamanda na rundunar “Operation Hadin Kai”, Christopher Musa, ya bayyana cewa adadin yan Boko Haram da suka mika wuya kawo yanzu ya kai 17,000.
Musa ya bayyana hakan ne ranar Juma'a lokacin da ya kai ziyara wajen shugabannin hukumar cigaban Arewa maso gabas, NEDC.
Ya bayyana cewa wannan adadi ya hada da mayaka, iyalansu da kuma wadanda aka tilasta shigar harkar Boko Haram.
Ya ce adadin masu mika wuyan na yawa kulli yaumin kuma hukumar na bukayar NEDC ta taimaka wajen kula da su.
A cewarsa, wannan kula da ake da su babban damuwa ne ga yan ta'addan ISWAP wadanda ke tunanin zasu gaji yaran Shekau da aka kashe.
Kwamanda Musa ya kara da cewa yan ta'addan ISWAP basu jin dadi kan mika wuyan da yan Boko Haram ke yi kuma haka ya sa suka kafa runduna ta musamman don hana mayaka guduwa.
Yace:
"Daga fadar shugaban kasa, Ministan tsaro, Shugaban hafsoshin tsaro, kowa na iyakan kokari don kawo karshen wannan matsala, kuma a samu zaman lafiya a Arewa maso gabas."
"Mun san idan aka samu zaman lafiya a Arewa maso gabas, sauran yankunan zasu amfana."
Ya jinjinawa hukumar bisa gudunmuwa da tallafin da suke badawa ga yankin kuma yayi kira da shugabanninta su duba yiwuwar hannunta wanann tallafi ga Sojoji musamman wajen gyaran gine-gine.
A nasa jawabin, Shugaban NEDC, Mohammed Alkali, ya jinjinawa kokarin Sojoji wajen samar da zaman lafiya a yankin.
Alkali ya baiwa Sojin tabbacin hadin kai da goyon baya.
Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai
Tiyata Kwamandan Manjo Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa yan Najeriya da duniya cewa za'a hukunta yan Boko Haram da suka mika wuya, ba zasu tsira daga hukuncin laifukan da suka yi ba.
A hirar da yayi da manema labarai a hedkwatar rundunar dake Maiduguri, Janar Musa yace babu wanda zai yafewa dubban yan ta'addan Boko Haram da suka aikata muggan laifuka irin wannan, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng