Zaben Gwamnan Anambra: Dan takaran APGA ya ce takaran APC mai garkuwa da mutane ne
- Dan takaran gwamnan jihar Anambra karkashin jam'iyyar APGA, Charles Soludo, ya daura babban kaulasa kan babban abokin hamayyarsa, Andy Uba na APC
- Soludo ya zargi dan takaran na APC da kwalin karatun Sakandare na bogi yake amfani da shi kuma ya taba garkuwa da wani tsohon gwamna
- Sanata Andy Uba kuwa ya karyata wannan zargi kuma ya bayyana yadda ya taimaki wanda ke sukarsa
Anambra - Dan takaran gwamnan jihar Anambra karkashin jam'iyyar APGA, Charles Soludo, ya tuhumi abokin hamayyarsa, Andy Uba na APC, da laifin amfani da kwalin bogi.
Hakazalika ya zargeshi da garkuwa da mutane, musamman na tsohon gwamnan jihar Chris Ngige.
Soludo ya bayyana hakan ne lokacin da yan takaran suka kara da juna a taron muhawaran da Arise News TV ta shirya kuma Legit.ng ta shaida ranar Litinin, 1 ga Nuwamba.
Charles Soludo wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN ne ya bayyana cewa:
"Ba kada takardan sakamakon jarabawar SSCE. Shin ka karbi kwalin kammala karatun sakandare a 1974, ka karba? Duk na bogi ne?"
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya zargeshi da garkuwa da mutane
Bayan haka, Soludo ya tuhumci Andy Uba da laifin kasancewa wanda ya shirya garkuwa da tsohon gwamnan jihar.
Uba ya musanta wandannan zargin.
Ya bayyana cewa sabanin yaki da Soludo, taimaka masa yayi har ya zama Gwamnan CBN.
Zaben gwamnan jihar zai gudana ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
Hukumar INEC ta fara rabon kayan zaben gwamnan jihar Anambra
Hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta fara rabon kayayyakin zaben gwamnan jihar Anambra da aka shirya yi ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba, 2021.
An fara rabon kayayyakin zuwa kananan hukumomin jihar 21, Legit ta ruwaito.
Jami'an hukumar INEC yanzu haka suna harabar hedkwatar bankin Najeriya CBN dake Anambra inda akayi ajiyan kayayyakin.
Wadanda ke hallare a wajen sun hada da wakilan jam'iyyun siyasa da kuma shugaban kwamitin yada labarai na INEC, Festus Okoye.
Asali: Legit.ng