Da Dumi: DSS, ICPC sun kama lakcarori 48 da jami'an tsaro, sun kuma gayyaci shugabannin jami'o'i 3
- ICPC da DSS sun kama lakcarori, jami'an tsaro da kwararru a fanin fasahar sadarwa da iyayen dalibai dss saboda magudin jarrabawa
- Hukumar yaki da rashawar ta ce wadanda aka kama din suna da hannu ne wurin magudi yayin rubuta jarrabawar hukumar sharen fagen shiga jami'o'i, (JUPEB)
- An kuma gayyaci shugannnin jami'o'i uku domin amsa tambayoyi game da rawar da suka taka yayin magudin jarrabawar da sakaci
Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ta kama wasu lakcarori kan zargin tafka magudi yayin jarrabawar hukumar sharen fage na shiga jami'o'i, JUPEB.
An kama su ne yayin wani samame da DSS da jami'an hukumar yaki da rashawa na ICPC suka kai kamar yadda yazo a sanarwar da ICPC ta fitar.
A yayin samamen da aka yi wa lakabi da 'Operation Combo' da aka yi tare da hadin gwiwar ma'aikatar ilimi ta tarayya, an kama lakcarori, ma'aikata, dalibai, da jami'an tsaro da ke da hannu a magudin jarrabawar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An gudanar da Operation Combo ne a jihohi bakwai bayan sanya idanu kan wasu makarantu da suka yi kwarin suna wurin magudin jarrabawar JUPEB.
An kuma kama shugaban makarantu masu koyar da dalibai da ke shirin rubuta jarrabawa, ATSO.
Makarantun da aka kai samamen
A cewar sanarwar da kakakin ICPC, Azuka Ogugua ta fitar, sanya idanu da bincike na tsawon lokaci ne ya bada nasarar kama wadanda ake zargin ciki har da iyayen dalibai.
Ogugua ta ce wadanda aka kama sun fito ne daga Jami'ar Wellspring, Benin, Jihar Edo; Jami'ar Christopher, Mowe, Jihar Ogun sai Jami'ar Crown Hill, Ilorin, Jihar Kwara.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Jami'an tsaron sun kuma kama wasu da ake zargi a cibiyoyin koyar da masu shirin rubuta jarrabawa da ke Jami'ar McPherson da Precious Cornerstone a Ibadan da Jami'ar Illara-Epe a jihar Oyo.
"Sahihan bayanai da aka tattara yayin samamen ya nuna iyayen dalibai na da hannu tsindum a harkar tare da mahukunta a jami'o'in."
Ana zargin shugabannin wasu jami'o'i da sakaci
Ta kuma yi bayanin cewa ICPC ta gayyaci a kalla shugannin wasu jami'o'i uku don yin bayani kan rawar da suka taka wurin magudin da sakaci wurin aikinsu na sanya ido.
Kakakin ta bayyana cewa masu magudin zaben suna amfani da dandalin sada zumunta ne wurin turawa dalibai tambayoyin jarrabawar kafin ranar jarrabawar bayan sun biya kudi.
Bincike ya nuna dalibai wasun su kananan yara kan biya N350,000 zuwa N500,000 a makarantun don magudin jarrabawar.
An bada belin wasu da ake zargin yayin da ake cigaba da bincike.
Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari
A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.
Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.
Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.
Asali: Legit.ng