Harin 'yan bindiga a UniAbuja: 'Yan sanda sun karyata rahoton ceto wadanda aka sace

Harin 'yan bindiga a UniAbuja: 'Yan sanda sun karyata rahoton ceto wadanda aka sace

  • Rundunar yan sandan birnin tarayya ta karyata batun ceto mutane shida da yan bindiga suka sace daga gidajen malaman jami'ar Abuja
  • An dai rahoto cewa wani ma'aikacin jami'ar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an yi nasarar ceto mutanen a yankin Abaji
  • Sai dai kuma mai magana da yawun rundunar yan sandan na FCT, Josephine Adeh ta fito ta karyata hakan inda ta nemi yan jarida da su daina watsa labaran karya

Abuja - Rundunar yan sandan birnin tarayya ta karyata rahotannin cewa an yi nasarar ceto mutane shida da yan bindiga suka yi garkuwa da su a gidajen malaman jami'ar Abuja.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan na FCT, Josephine Adeh ce ta bayyana hakan, gidan talbijin na AIT ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin jami’ar Abuja

Harin 'yan bindiga a UniAbuja: 'Yan sanda sun karyata rahoton ceto wadanda aka sace
Harin 'yan bindiga a UniAbuja: 'Yan sanda sun karyata rahoton ceto wadanda aka sace Hoto: UNIABUJA
Asali: Facebook

Adeh wacce ke martani ga wani sashi na labarai da ya nakalto wani ma'aikacin jami'ar yana tabbatar da ceto mutanen a Abaji, hanyar babban titin Abuja-Lokja da taimakon yan sanda da yan banga ta bukaci yan jarida da su guji yada labaran karya.

Rahoton ya kuma kawo cewa da aka tuntube shi, kakakin jami'ar Abuja, Habib Yakoob, ya ce ba zai iya tabbatar da gaskiyar ikirarin ma'aikacin da ya nemi a boye sunansa ba.

Da farko dai mun ji cewa an samu labaran cewa mutum shida da yan bindiga suka sace a Jami'ar birnin tarayya Abuja sun samu kubuta.

The Sun ta ruwaito wani ma'aikaci a jami'ar da ya tabbatar da maganar cewa an ganosu ne a garin Abaji, kan babban titin Abuja-Lokaja, bisa taimakon jami'an yan sanda da bijilanti. Yanzu haka suna ofishin yan sandan Abaji.

Kara karanta wannan

Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda

Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja SQ, sun kwashe ma'aikata da 'yayansu

A baya mun kawo cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidajen Malaman jami'ar Abuja (UniAbuja) cikin daren Talata, 2 ga watan Nuwamba 2021 kuma sun yi awon gaba da mutane.

Legit Hausa ta tattaro cewa yan bindiga sun dira gidajen ne dake unguwar Giri, hanyar zuwa tashar jirgin sama Gwagwalada, Abuja. An sace wani Farfesa Oboskolo, wanda ke tsangayar Ilimi a jami'ar.

Hakazalika Jami'ar ta bayyana cewa tuni an tura jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro a wajen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel