Jerin sunayen mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin jami’ar Abuja
- An saki sunayen mutanen da 'yan bindiga suka sace a harin da suka kai jami'ar Abuja a safiyar yau Talata
- Daga cikin mutane shida da aka sace akwai farfesoshi biyu, wani babban ma'aikaci da kuma yaransu
- Wani ma'aikacin jami'ar da ya magantu kan lamarin, ya ce yanayin da maharan suka aiwatar da farmakin nasu ya nuna cewa sun yi bincike sosai kafin zuwan su
Abuja - Wani rahoton Channels TV ya nuna cewa akwai farfesoshi guda biyu a cikin mutane shida da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jami'ar Abuja a safiyar ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba.
Legit Hausa ta rahoto yadda 'yan bindiga suka kai hari kwatas din malaman da ke GIRI, yankin Gwagwalada na babbar birnin tarayya.
Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto cewa wani babban ma'aikacin jami'ar ya bayyana sunayen mutanen da aka sace a harin.
Ga jerin sunayen nasu
1. Farfesa Bassey Ubom
2. Diyar Farfesa Bassey Ubom
3. Dan Farfesa Bassey Ubom
4. Farfesa Obanza Malam
5. Sambo Mohammed
6. Dr. Tobit
Ubom, wanda ya kasance Farfesa a fannin Kimiyya da Ilimin Muhalli, yana koyar da Kimiyyar Muhalli a Jami'ar.
Ma'aikacin ya ce duba ga yanayin da miyagun suka aiwatar da ta'asarsu, ya nuna karara cewa sun gudanar da bincike sosai kafin suka kai farmakin.
A yanzu haka, wata tawagar hadin gwiwa na jami'an yan sanda da sojoji suna gudanar da aikin kakkaba a yankunan Gwagwalada domin ceto wadanda aka sace.
Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda
A baya mun kawo cewa hukumar 'yan sandan babbar birnin tarayya ta tabbatar da cewar 'yan bindiga sun yi awon gaba da akalla ma'aikatan jami'ar Abuja su shida, rahoton Daily Trust.
A cikin wata sanarwa, kwamishinan yan sandan birnin tarayya, Babaji Sunday, ya ce ya tura karin kayan aiki na yan sanda zuwa harabar jami'ar ta Abuja, rahoton Premium Times.
Ya kuma bayyana cewa ya umurci jami’an da su kula da bangaren kwanan ma’aikata da sauran bangarorin jami’ar, domin karfafa tsaro, inganta lafiyar jama’a da kuma kare jama’a a ciki da kewayen jami’ar.
Asali: Legit.ng