Wasu iyaye na cin zarafin 'ya'yansu: Ganduje ya koka kan iyaye masu tura 'ya'yansu bara
- Gwamna Ganduje ya koka kan yadda iyaye ke tilastawa'ya'yansu barace-barace a Arewacin Najeriya
- Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin mummunan abu, Kuma hakan cin zarafin yara ne kanana
- Gwamnan a kasafin kudin 2022, ya ware makudan kudade don tallafawa harkar ilimi a jihar Kano
Kano - Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan mugun halin wasu iyaye a yankin arewacin kasar nan da ke tilastawa 'ya'yan su barace-barace yana mai bayyana hakan a matsayin cin zarafi.
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa lokaci ya yi da dokokin tarayya za su kara kaimi wajen kafa dokar hana barace-barace a duk sassan kasar nan, jaridar Leadership ta ruwaito.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin taron kasa karo na biyu da tsangayar ilimi ta Jami’ar Bayero da ke Kano ta shirya, ya bayyana cewa dokar za ta tilastawa iyaye/iyayen riko su saka ‘ya’yansu a makaranta.
Ya kara da cewa kalubalen tsaro da ayyukan ta’addanci sun haifar da karin matsaloli a bangaren ilimi a yankin Arewa maso Gabas da wasu jihohin Arewa maso yammacin kasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban taron Farfesa Abdulrasheed Garba ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta ware sama da 26% na kasafin kudinta na 2022 ga fannin ilimi, sannan ya bukaci sauran gwamnatocin jihohi su yi koyi da hakan.
Gwamna Ganduje ya jima yana fada da yawaitar barace-barace a Arewacin Najeriya, musamman jiharsa ta Kano.
A shekarar 2020, jaridar Punch ta ruwaito yadda gwamnan ya Hana barace-barace a jihar Kano ba ga yara kadai ba, har ma ga masu manyan shekaru.
Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno
A wani labarin, Kungiyar Tarayyar Turai ta hanyar shirye-shiryenta na tallafi ta farfado da rayuwar miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihohin Borno da Arewa maso Gabas, in ji shugabar tawagarta a Najeriya da ECOWAS, Ambasada Samuela Isopi.
Ta ce kungiyar ta EU ta bada kudi kusan Yuro miliyan 130 a cikin shekaru hudu da suka gabata don tallafawa kokarin gwamnatin jihar Borno na sake ginawa da kuma gyara al’ummomin da abin ya shafa, Leadership ta ruwaito.
Wannan tallafin kudade kadai, a cewarta, ya taimaka wajen maido da ababen more rayuwa a fannoni da yawa.
Asali: Legit.ng