Da Dumi: An tsinci gawar ƴan bindiga 3 da suka kashe kansu wurin faɗan rabon kuɗin fansa a wata jihar Arewa

Da Dumi: An tsinci gawar ƴan bindiga 3 da suka kashe kansu wurin faɗan rabon kuɗin fansa a wata jihar Arewa

  • An tsinci gawarwakin wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne da suka mutu yayin fadan rabon kudin fansa a Taraba
  • Mutanen wani gari da ke kusa da dutse a karamar hukumar Ardo sun tabbatar da cewa masu garkuwan sun dade suna zaune a kan dutsen
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi ya ce ba su samu rahoton aukuwar lamarin ba amma idan da gaske ne labari ne mai dadi

Taraba - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun rasa rayyukansu yayin fada kan kudin fansa a jihar Taraba kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

Lamarin, a cewar majiyoyi ya faru ne kwanaki kadan bayan an biya su kudin fansa mai yawa saboda sace wani dan kasuwa da matarsa da suka yi a Jalingo makonni kadan da suke wuce.

Kara karanta wannan

Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa

Da Ɗuminsa: An gano gawarwakin masu garkuwa 3 da suka yi faɗa kan kuɗin fansa a Taraba
An gano gawarwakin masu garkuwa 3 da suka yi faɗa kan kuɗin fansa a Taraba. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa sun yi fadan ne a kusa da wani dutse da ke karamar hukumar Ardo Kola a jihar Taraba.

Majiyoyi sun ce mazauna kauyen da ke zaune kusa da duwatsun sun ji muryoyi na tasowa daga dutsen da masu garkuwar suka yi kaka gida a can.

Ya ce an tsinci gawarwaki uku a wurare daban-daban a dutsen.

Majiyar ta ce:

"Masu garkuwa da mutanen sun yi fada da junansu kuma wasu sun mutu. Hakan ya faru ne yayin rabon kudin fansa amma wannan ne lokaci na farko da aka tsinci gawarwaki."

Masu garkuwan suna bi ta Kogin Mallam Garba domin zuwa mabuyarsu da ke dutsen Kwando.

Sun sha yi wa mazauna kauyen gargadin cewa kada su sake su fada wa jami'an tsaro cewa suna ganinsu a wurin.

Kara karanta wannan

Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara

Majiyar ya kara da cewa:

"Masu garkuwar suna harkokinsu a yankin; su kan zo a kan babura kuma wasu lokutan a kan kawo musu kudin fansa a dajin da ke kusa da wurin, mafi yawanci cikin dare."

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi ya ce ba su samu rahoton aukuwar lamarin ba.

Ya ce:

"Zan bincika sanan in sanar da ku. Amma idan da gaske masu garkuwa sun kashe kansu, wannan labari ne mai dadi."

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Ƴan bindiga sun gargaɗi sojoji su fice daga wani gari a Filato domin za su kawo hari

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164