Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara
- Shugaban yan bindiga, Dogo Gide, ya haramta shan giya da kwayoyi da kayan maye a wasu kauyukan jihar Zamfara
- Hakan na zuwa ne bayan Gide ya kwace kwayoyi daga hannun dilallai ya kona ya kuma mayar musu da kudinsu
- Gide ya gargadi mutanen gari da yaransa cewa duk wanda aka samu yana sha ko sayar da kayan mayen za a hallaka shi a bainar jama'a
Zamfara - Dogo Gide, hatsabibin dan bindiga, ya saka dokar hana siye da siyar da giya da sauran muggan kwayoyi a wasu garuruwan masarautan Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Shugaban 'yan bindigan da ke zaune a dajin Kuyambana, da ya ratsa ta jihohin Zamfara, Kaduna, Niger da Kebbi ya kwace iko a garin Babbar Doka, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A satin da ya gabata, yaran sa sun kashe wani shugaban yan bindigan da ake kira Damina.
Ya gargadi mazauna kauyukan cewa a bainar jama'a za a kashe duk wanda aka kama yana sayar da miyagun kwayoyi ko kuma shan su.
Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa tunda farko Gide ya kwace miyagun kwayoyi daga wasu da ake zargin dillalai ne sannan ya cinna musu wuta.
Ya kuma kidaya kudin kwayoyin ya biya wadanda suka yi safarar su, ya gargadi yaransa da sauran yan kauyen su dena shan miyagun kwayoyin.
Majiyar ta kara da cewa:
"An kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi ciki har da wani Zakin Goro a yayin da aka kai sumame gidan masu kwarmatawa yan bindiga bayanai.
"Wasu lokutan, bata garin na zuwa shagunan sayar da magani su siya miyagun kwayoyin. Su kan yi wa kansu allurar Pantazocine su tafi bayan shan wasu kwayoyi irin su Tramadol da sauransu.
"Amma yan bindiga suna yawan siyan wani allura mai suna Pentazocine kuma ana dillalan miyagun kwayoyin da suka zama masu kai wa yan bindiga bayanai ke kai musu cikin daji."
Abin da shugaban kungiyar likitocin Nigeria na Zamfara ya ce game da Pentazocine
Shugaban kungiya likitocin Nigeria a Zamfara, Dr Mannir Bature ya ce Pentazocine maganin kashe ciwon jiki ne mai karfi da aka bawa marasa lafiya ta jijiya amma bata garin na amfani da shi ba bisa ka'ida ba.
Ya ce Pentazocine yana rage wa marasa lafiya jin zafi musamman wadanda za a yi wa tiyata saboda ya rage musu radadi a yayin aikin.
Ya ce wasu lokutan maganin yana saka maye ko gane-gane ga wadanda suke amfani da shi ba bisa ka'ida ba.
Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
A jiya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.
A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.
Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.
Asali: Legit.ng