Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

  • Ana sa ran jin yadda za ta kaya a shari'ar Abba Kyari na zargin badakala da hannu a damfara wani balarabe
  • A halin da ake ciki, an dakatar da Abba Kyari daga aikinsa bisa zarginsa da karbar kason damfarar da Hushpuppi ya yi
  • Kwamitin ladabtarwa na rundunar zai fitar da rahoton shawarwarin da yanke kan makomai Kyari nan kusa

Abuja - Punch ta ruwaito cewa, makomar tsohon kwamandan tawagar IRT ta 'yan sanda, Abba Kyari, na nan tafe, a daidai lokacin da hukumar ‘yan sanda ke jiran shawarwarin kwamitin ladabtarwa na rundunar ‘yan sanda kan shari’ar sa.

An tattaro cewa shawarwarin FDC za su kasance jigon hukuncin da hukumar za ta yanke tare da tabbatar da makomar Kyari a aikin dan sandan Najeriya.

Batun Abba Kyari: Saura kiris duniya ta san gaskiya abin da ake ciki, FDC zai ba da rahoto
Jami'in dan sanda Abba Kyari | Hoto: Abba Kyari
Asali: Facebook

Kwanakin baya rahotanni sun bayyana cewa, Sufeto Janar na 'yan sanda ya mika bayanan bincike kan zargin Abba Kyari da hannu a cikin badakalar dala miliyan 1.1 kan wani balarabe tare da Hushpuppi ga ministan shari'a Abubakar Malami (SAN).

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Rahoton ya kunshi bayanan kara da shaidu da sakamakon bincike da kuma shaidun Kyari da sauran mutane da kungiyoyin da ke da alaka da lamarin.

Wani wakilin FBI, Andrew Innocenti ne ke bincike tare da yin kai kawo a lamarin a wani kotun Amurka kan batun badakalar.

Hukumar ta FBI ta kuma ce Hushpuppi ya tura dala 20,600 a asusun banki da Kyari ya bashi.

Don haka kotun ta bayar da umarnin a tsare Kyari na tsawon kwanaki 10.

Hushpuppi ya amsa laifin satar kudade kuma ana sa ran zai shafe shekaru 20 a gidan yari.

Za a sanya ranar da za a yanke wa Hushpuppi hukunci domin sanin tsawon lokacin da zai yi a gidan yari.

A bangaren Kyari, an dakatar da Kyari daga aiki ne a ranar 31 ga watan Yuli sakamakon zarginsa da hannu a zambar. Ya kuma bayyana a gaban SIP.

Kara karanta wannan

EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa bayan kwashe kwana 2 a hannun ta

Shugaban SIP, Joseph Egbunike, mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, ya mika rahoton binciken kwamitin ga IGP a ranar 26 ga watan Agusta, a hedikwatar rundunar da ke Abuja, kwanaki 24 bayan kaddamar da kwamitin.

Da yake bayar da karin haske kan lamarin a ranar Laraba, wani babban jami’i ya bayyana cewa, Kyari ya amsa kiran da FDC ta yi masa.

Ya kara da cewa ana sa ran kwamitin zai fitar da shawarwari dangane da martanin da ya bayar da kuma hujjojin da ke kunshe cikin rahoton na SIP.

Sai dai, a baya, ministan 'yan sanda ya bayyana cewa, shugaba Buhari ke da maganar karshe kan batun na Abba Kyari, Vanguard ta ruwaito.

Bincike ya nuna irin sassaucin da za a yiwa Abba Kyari amma zai fuskanci kora

A baya kuwa, an ce akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa Abba Kyari dake fuskantar gurfana a Kotun Gundumar California ta Amurka bisa zarginsa da hannu a wata damfara ta shahararren dan damfara, Ramon Abbas (Hushpuppi), na iya samun sassaucin hukunci daga hukuma, in ji jaridar This Day.

Kara karanta wannan

Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana a kotu kan zargin damfarar yanar gizo

Abba Kyari, wanda ya kasance mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban shugaban wata rundunar fikira ta IRT a Najeriya.

An dakatar da Abba Kyari yayin da aka fara gudanar bincike kan lamurran da suka faru tsakaninsa da Hushpuppi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.