EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa bayan kwashe kwana 2 a hannun ta
- Hukumar EFCC ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, bayan kwanaki biyu da yayi a hannun ta
- Kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, an tsare Anyim ne sakamakon badakalar wasu kudi da suka kai N780 miliyan
- Kudaden suna da alaka da Sanata Stella Oduah kuma an waskar da su ne zuwa wani kamfani da Anyim ya ke da hannun jari a ciki
Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta sako tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, bayan an titsiye shi na kwanaki biyu kan zargin rashawa.
Lauyansa, Mike Ozekhome ne ya sanar da Premium Times hakan a ranar Laraba.
Hukumar ta tsare Anyim tun daga ranar Lahadi kuma aka sako shi kan belinsa da hukumar ta bayar a ranar Talata, kamar yadda Ozekhome, SAN, ya sanar.
Tsohon shugaban majalisar dattawan tsakanin 2000 da 2003, wanda yayi aiki daga bisani a matsayin sakataren tarayya karkashin Goodluck Jonathan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An garkame shi a hedkwatar hukumar da ke Abuja tun daga wurin karfe 3 na yammacin ranar Lahadi.
An tuhume shi kan wata harkalla ne da ta shafa sanatar Stella Oduah mai wakiltar Anambra ta Arewa a hukumar kamar yadda majiyoyi suka sanar da Premium Times.
Majiyoyin sun ce hukumar ta gayyaci tsohon shugaban majalisar kan wani zargin waskar da wasu kudade da ya hada da Odua wadanda suka kai N780 miliyan.
Ana zargin an waskar da kudaden ne zuwa wani kamfani wanda ake zargin tsohon dan majalisar ya na da ruwa a ciki.
Oduah tsohuwar ministan sufurin jiragen sama ce karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga 2011 zuwa 2014. An sallame ta a wancan lokacin bayan kwangilar damfara da ta bada ta siyan wasu motoci kirar BMW wadanda harsashi ba ya hudawa.
EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m
A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, reshen Ibadan a ranar Talata, ta gurfanar da yariman Owo, Touluwalade Olagbegi.
An gurfanar da yariman a gaban mai shari'a Uche Agomoh a babbar kotun tarayya da ke zama a Ibadan kan laifin samun kudi har miliyan talatin da biyar ta hanyar karya.
Ana zargin yariman Owo na jihar Ondo, wanda ke zama a Bodijia, da karbar kudi har N35 miliyan daga mai korafin kan cewa za su yi kasuwancin forex, EFCC ta wallafa a shafin ta na Facebook.
Asali: Legit.ng