Zaben Anambra: IGP ya tura manyan 'yan sanda sama da 100 kan barazanar IPOB
- Kafin isowar zaben gwamnonin jihar Anambra, IGP Usman Baba Alkali ya tura manyan 'yan sanda a kalla 100
- Hakan ya biyo bayan barazanar da 'yan awaren IPOB suka yi na tabbatar da sai sun hargitsa zaben gwamnonin
- Akwai mataimakan sifeta janar na 'yan sanda 4, kwamishinoni 31 da sauran manyan 'yan sanda da aka tura
Anambra - Kafin zuwan zaben gwamnoni na 6 ga watan Nuwamba a jihar Anambra, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya aike a kalla manyan jami'an 'yan sanda dari domin samar da tsaro isasshe a jihar.
Wannan na zuwa ne ana tsaka da tsoro tare da fargabar barazanar da 'yan awaren IPOB ke yi na hargitsa zaben, Daily Trust ta wallafa.
Daga cikin jami'an 'yan sanda da aka tura jihar Anambra akwai mataimakan sifeta janar na 'yan sanda 4, kwamishinonin 'yan sanda 14, mataimakan kwamishinonin 'yan sanda 31 da kuma wasu manyan jami'ai 48.
Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG
Kamar yadda takardar da kakakin rundunar, Frank Mba ya fitar, ya ce 'yan sandan za su samu shugabancin DIG na FCID, Joseph Egbunike.
Kamar yadda yace, Egbunike ke da alhakin kula da dukkan ayyukan tsaro a yayin zaben domin tabbatar da an yi zaben cikin lumana.
Ya kara da cewa, Egbunike zai samu taimakon DIG na ayyuka, DIG Zaki Ahmed, Daily Trust ta wallafa.
Shugaban 'yan sandan ya ce suna tabbatar wa da jama'ar kasar nan cewa rundunar ta shirya tsaf domin zaben gwamnonin.
Ya yi kira ga jama'ar jihar Anambra da su fito kwan su da kwarkwatarsu wurin sauke hakkin da ke kansu domin za a samar da isasshen tsaro kafin, yayin da bayan zaben.
Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB
A wani labari na daban, Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin kungiyar 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB).
Ya sanar da hakan ne yayin martani kan caccaka mai zafin da wata jaridar London, The Economist ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa.
Jaridar ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ta ce mulkinsa ya gaza shawo kan rashawa, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng