Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kauyen na jihar Neja
  • Sun hallaka mutane da yawa yayin da suke gabatar da sallar Asuba, inda kuma suka jikkata wasu
  • Gwamnatin jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, tare da bayyana daukar mataki akai

Neja - Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Maza-Kuka da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja, inda suka kashe wasu masallata 18.

An tattaro cewa, ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne da yawan gaske inda suka far wa mutanen kauyen da ke gudanar da sallar asuba.

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja
Taswirar jihar Neja | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim-Matane ya tabbatar wa jaridar The Nation faruwar harin.

Ya ce an kashe mutane 16 a masallacin nan take yayin da aka kashe daya a kauyen Kaboji a wani harin na daban.

Kara karanta wannan

Karin bayani: ISWAP ta hallaka wasu jiga-jigan kwamandojin Boko Haram da mabiyansu 18

Mista Matane ya ce gwamnatin jihar ta Neja ta tura tawagar jami’an tsaro zuwa dajin domin bin diddigin ‘yan bindigar.

Hakazalika, shugaban karamar hukumar Mashegu, Alhassan Isa Maza-Kuka shi ma ya tabbatar da faruwar wannan barna, inda ya bayyana shi a matsayin abin da ya yi matukar tayar da hankalin jama’a.

A karshe an garzaya da wanda ya ji rauni zuwa wani asibiti da ke Minna domin ba shi taimakon gaggawa.

Yadda 'yan fashi suka harbi mai shagon POS saboda kin basu kudi cikin dadin rai

A wani labarin, 'Yan fashi da makami sun harbi wata mai sana'ar cire kudi da POS mai suna Dorcas a tashar Alade Mega da ke Garin Ogbomoso, Jihar Oyo a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa SaharaReporters cewa 'yan fashin sun isa shagon da misalin karfe 8 na dare lokacin da sauran ma'aikata suka kawo cinikinsu na yau da kullum zuwa hedikwatar kamfanin.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

Ta bayyana cewa lokacin da mutanen uku dauke da makamai suka isa shagon, sun gabatar da kansu a matsayin ‘yan fashi, kuma sun nemi mai aikin da ta fito da dukkan kudin da ke shagon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.