Rundunar ‘yan sanda ta yi ram da wasu mutum 19 da ake zargi da aikata laifuka a jihar Bauchi
- 'Yan sanda a jihar Bauchi sun damke wasu mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar
- Laifukan da ake zargin su da aikatawa sun hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, sata, hada baki da kisa
- Kakakin 'yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba
Jihar Bauchi - Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta ce ta kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar cikin watanni biyu da suka gabata.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Wakil, ya fitar a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba.
Wakil ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne kan laifuka mabanbanta kuma a wurare daban-daban a fadin jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.
Ya bayyana laifukan wadanda suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, sata, hada baki da kisa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin rundunar ya kara da cewa sun samo bindigar AK-47, muggan makamai, na’urar laftop, wayoyin salula da wani babur daga hannun wadanda ake zargin.
Wakil ya ce sun yi kamun ne bayan samun bayanan sirri da kuma amfani da dabarun ‘yan sandan jiha.
Ya ce an tattara bayanai kan wadanda ake zargin kuma za a tura su kotu da zaran an kammala bincike, jaridar Punch ta kuma rahoto.
Yayin da yake sake jaddada jajircewar rundunar don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, Wakil ya bukaci mutane da su hada kai da 'yan sanda ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan mutanen da ke nuna rashin gaskiya,
Sannan ya nemi su kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba a garuruwansu.
Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi
A wani labarin, rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Enoch Yohanna bisa zargin ture budurwarsa, Ruth Amos har lahira.
Kakakin ‘yan sandan na jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba, ya ce wasu jami’ai da ke sintiri, sun gano budurwa kwance malele cikin jini, rahoton The Nation.
Hakazalika sun same ta da raunuka a kanta sannan jini na ta bulbulowa daga bakinta a yankin Sabon Kaura da ke garin Bauchi.
Asali: Legit.ng